Nijeriya za ta fi Indiya cin gajiyar kasuwancin fasaha a nan gaba, inji NITDA

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Hukumar Bunƙasa Ilimin Fasahar Zamani NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana cewa shirye-shiryen hukumar wajen bunƙasa kasuwanci ta fuskar amfani da kafofin intanet a Nijeriya sun yi nisa, inda Nijeriya za ta zarta Indiya damar kasuwancin fasahar zamani.

Babban Daraktan ya shaida haka ne ga manema labarai a babban ofishin hukumar dake Abuja, a yayin da yake bayyana matakan da hukumar ke ɗauka don ganin Nijeriya ta bi sahun ƙasashen duniya a fanin kimiyya da fasahar zamani a ɓangaren kasuwanci.

Ya ce hukumar ta zo da wani tsari da ake kira ‘Strategic Roadmap’ wanda yake taka rawa wajen canja harkar fasahar zamani a ƙasar nan cikin sauri. Ya ce tsari ne dake ɗauke da taswirori guda huɗu, wanda aka fara daga shekara ta 2016.

Malam Kashifu ya ce hukumar ta fitar da bincike guda 7 waɗanda za su ɗora Nijeriya a kan harkar tattalin arziki na zamani wato “Digital Economy”.

Tsare-tsaren sun haɗa da Developmental Regulation, dokar da za ta taimaka wa ’yan ƙasa wajen gane abubuwan da ya kamata su yi da fasashar zamani, lamarin da zai ba su damar samun cigaban tattalin arziki cikin kasuwancin nasu cikin sauri.
Akwai kuma dokar ‘Nigeria Data Protection Regulation’ wadda ta ke tantance irin bayanan da suka dace mutane su ɗora a yanar gizo don bunƙasa kasuwancin su.

A vangaren kasuwar wannan harkar a yanzu ta haura naira bilyan 2, sannan daga ciki hukumar na zuwa da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, da kuma waɗanda za su taimaka wajen tabbatar da an yi ayyuka daidai a gwamnatance.

“Ko a kwanan nan akwai tsarin da muka fitar wanda ’yan ƙasa za su ci gajiyar shi, inda za su iya samun aiki a wata qasa kuma su gabatar da shi alhalin suna nan Nijeriya wajen amfani da yanar gizo.

“Manufar wannan tsarin shi ne saboda Indiya a duniya ita ta mamaye wannan kasuwancin, sai mu ka ga ai Nijeriya ta fi Indiya dama, saboda lokacin mu ya fi kusa da Amurka da Turai a kan lokacin Indiya, na biyu Nijeriya ta fi mutanen da suka iya turanci, saboda yanzu ƙasar Indiya ma waɗanda suka iya turanci suna raguwa, saboda haka muka fitar da tsarin yadda za a yi Najeriya ta mori wannan tsari.

“Akwai kuma tsarin ‘Digital Capacity Building’, saboda harkokin fasahar zamani sai da ilimi, don  haka akwai horas wa da muke yi wa mutane akan fannoni daban-daban, wanda a cikin shekara 1, NITDA ta horar da mutum 40,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *