01
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta kafa dokar kulle ba don yaƙi da cutar korona. Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da jami'ai na musamman su 2000 kan yaƙi da cutar korona a jihar wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar a Lahadin da ta gabata. Idan dai za a iya tunawa, ko a bara gwamnatin Kano ta kafa dokar kulle a jihar a matsayin wani mataki na daƙile yaɗuwar korona. Da yake magana yayin ƙaddamarwar, Gwamna Ganduje ya ce, "Gwamnati ba ta ga dacewar sake sanya dokar…
