Wataƙila cutar korona ta zama silar hana attajirai zuwa asibiti a ƙetare – Ume

Daga WAKILIN MU

Wani Babban Lauyan Nijeriya kuma tsohon Babban Lauyan Jihar Imo, Chukwuma-Machukwu Ume ya ce, annobar korona ta ɗan taki wani matsayi na a yaba mata saboda tasirin da ta yi na kusa kawo ƙarshen bulaguron da wasu masu ƙumbar susa kan yi zuwa ƙasashen ƙetare don jinya.

Ume ya ce, duba da yadda annobar ke ta yaɗuwa kamar wutar daji, hakan zai tilasta wa shugabannin siyasar Nijeriya gina manya asibitoci masu inganci kwatankwacin na sauran ƙasashen duniya da suka cigaba don kula da lafiyar al’umma.

Waɗannan bayanai da Ume ya yi, suna ƙunshe ne cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai a wannan Lahadin.

Lauyan ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci a kan aikin gina asibitin koyarwa ta zamani ta Jihar Ebonyi da ke kan gudana a yankin Uburu.

Inda ya yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa Gwamnan Jihar Ebonyi, Engr. Dave Umahi, dangane da ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa walwalar al’umar jiharsa.

Yana mai cewa, “Bayan kammala asibitin, za ta zama asibiti mafi inganci a nahiyar Afirka.

“Duba da yadda al’amura ke tafiya, maiyiwuwa annobar korona ta ƙare da samun yabo. Saboda tuni wasu shugabanni a Nijeriya sun soma nazarin daina tafiya ƙetare neman magani.”

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna cewa, asibitin wanda aikin gina ta ya kai kashi 75 cikin 100, bayan kammalawa tana da ƙarfin kula da masu fama da cutar daji da cutar ƙoda da tarin fuka da cututtuka masu alaƙa da zuciya da dai sauransu.

Idan dai za a iya tuwana, a baya jaridar Manhaja ta ruwaito hamshaƙin mai kuɗin nan na ƙasar Amurka, Bill Gates, na cewa, akwai buƙatar Nijeriya ta bada muhimmanci sosai wajen inganta tsarin kula da lafiya a matakin farko don iya fuskantar ƙalubalen da duniya ke fuskanta.