Bankin Zenith ya ciri tuta

Daga FATUHU MUSTAPHA

A karo na huɗu a jere, bankin Zenith ya sake zama bankin da ya ɗara takwarorinsa ingancin tsarin gudanarwa a Nijeriya kamar yadda mujallar Banker Magazine ta nuna.

Daga jerin bankuna ‘yan sahun gaba su 500 da mujallar ta nuna a 2021, ta ayyana Bankin Zenith a matsayin bankin da ke kan gaba wajen tsarin aiki a Nijeriya.

Mujallar ta nuna cewa, ƙarfin jarin Bankin Zenith ya kai Dalar Amurka milyan 275 wanda hakan ya sa ya zama bankin da ya samu cigaba daga matsayi na 392 a 2020 zuwa matsayi na 390 a 2021 a matakin duniya.

A cewar Mujallar, Bankin Zenith ne kaɗai daga Nijeriya ya samu shiga sahun bankuna 400 na farko mafi inganci a duniya.

Mujallar ta wallafa bayanan matakan bankunan ne a fitowarta ta Fabrairun 2021.

Da yake tsokaci kan cigaban da bankinsu ya samu, Shugaban Bankin Zenith, Mr. Ebenezer Onyeagwu ya bayyana cewa, “Wannan na nuna irin ƙwazon da bankin ke da shi wajen gudanar da harkokinsa duk da irin ƙalubalen da annobar korona ta haifar.

“Bankin Zenith zai ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata wanda hakan ya sa ya zama kan gaba a tsakanin takwarorinsa a Nijeriya.”

Ko a baya, bankin ya samu shaidar yabo da dama a wurare daban-daban sakamakon aiki bil haƙƙi da yakan yi.