Gwamnati ta amince da batun buɗe sabbin jami’o’i 20 a faɗin ƙasa

Daga AISHA ASAS

Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ta aminta da batun samar da sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 20 a faɗin ƙasa.

Majalisar ta cim ma wannan matsaya ne yayin zamanta na Larabar da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya ce, jami’o’in za su samu lasisin zarafin gudanarwa ne daga hannun Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), wanda za su yi amfani da shi nan da shekaru uku masu zuwa, yayin da gwamnati za ta ci gaba da sanya musu ido.

Jami’o’in da Majalisar ta amince da a kafa ɗin sun haɗa da Topfaith University, Mkpatak a jihar Akwa Ibom, da Thomas Adewumi University, Oko-Irese, a jihar Kwara, da Maranathan University, Mgbidi a jihar Imo, da Ave Maria University, Piyanko a jihar Nasarawa.

Sai kuma Al-Istiqama University, Sumaila a jihar Kano, da James Hope University, Lagos a jihar Lagos, da Maryam Abacha American University a Kano da dai sauransu.

Yana da kyau a fahimce cewa, 9 daga cikin jami’o’in da aka amince da kafawar suna yankin Arewa ta tsakiya ne, sannan 3 a yankin Kudu maso-kudu, yayin da shiyyar Kudu maso-gabas ke da guda 2, shi kuwa yankin Arewa maso-yamma na da 5, sai kuma 1 a Kudu maso-yamma.