NCDC ta samar da lambar tantance sahihancin bayanai

Daga AISHA ASAS

A matsayin wani mataki na sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya iya tantance sahihancin bayanai game da cutar korona, Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) tare da taimakon Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), ta samar da lamba ta musamman da za ya taimaka wa ‘yan ƙasa wajen tantance bayanai.

NCDC ta ce, a duk lokacin da buƙatar neman tabbatar da sahihancin wani bayani ta taso, ‘yan ƙasa na iya kiran lambar “6232” don tabbatar da ingancin wani bayani a kan korona da sauran cututtuka.

A bayanin da Babban Daraktan NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu, ya yi a Larabar da ta gabata a Abuja, ya ce kiran lambar kyauta ne ga kowa, ga kuma sauƙin haddacewa.

“An yi wannan ne domin samar wa ‘yan Nijeriya hanya mai sauƙi wajen tantance bayanai dangane da cututtuka masu yaɗuwa”, inji Ihekweazu.

Kazalika, ya ce NCDC ta cim ma wannan hanya ne tare da taimakon takwarorinta dagda ɓangarori daban-daban.