Fulani na da ‘yancin zama ko’ina a Nijeriya – Ƙungiyar Igbo

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Gamayyar Ma’aikata ‘Yan Kudu Maso-gabas a Nijeriya da Ƙetare (CSEPNND), sun yi tir da ayyukan ‘yan ƙungiyar IPOB ƙarƙashin jagorancin Nnamdi Kanu, musamman ma la’akari da yadda suke muzguna wa Fulani makiyaya a shiyarsu.

A wata takardar bayani da shugaban ƙungiyar, Prof. Madumere Chika, ya fitar a ranar Alhamis wadda Jaridar Manhaja ta samu kwafinta, Chika ya ce Fulani makiyaya na da ‘yancin zama ko’ina a faɗin Nijeriya ba tare da fuskantar muzgunawa ba kamar dai yadda Kundin Dokokin Ƙasa na 1999 ya nuna.

Ƙungiyar ta cacciki Kanu da mabiyansa kan cewa sun sa ana yi wa ƙabilar Igbo kallon jma’a masu son rikici waɗanda ba su son baƙi da zaman lafiya a ƙasa.

CSEPNND ta yi tunatarwa ga ƙabilar Igbo na gida da ƙetare kan cewa su sani a baya kotu ta bayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda tare da yin tir da shirin bada tsaron da Kanu ya samar, wato ‘Eastern Security Network’, ko kuma ESN a taƙaice, tana mai cewa babu yadda za a yi a samu sarki biyu a gari guda.

Ƙungiyar ta yi kira ga sojoji da sauran hukumomin tsaro da su je su tattara dukkan waɗanda ke gudanar da shirin bada tsaro assasawar Kanu a shiyyarsu, sannan a tsarwatsa shirin baki ɗayansa.

A hannu guda, ƙungiyar ta yaba wa Hausa/Fulani mazauna yankin bisa yadda ba su yarda sun ɗauki doka a hannunsu ba duk da irin muzgunawar da mabiyan Kanu suka yi musu.