Babu abin da zai cika sai da mace a ciki – Hajiya Halima

Hajiya Halima Idris ita ce Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, a fannin Fikira da Ƙirƙira. Ta yi fice ta fuskoki da dama tun gabanin muƙamin ta, musamman wajen kishin Arewa da son cigaban mata da matasa. A wannan hirar da wakiliyar manhaja, AISAH ASAS, ta  yi da Halima Idris, ta bayyana abubuwa da dama da suka haɗa da ayyukan ta  a gwamnati da kuma fannin kwalliya. Ga yadda hirar ta kasance:

Kin yi fice a harkokin cigaban matasa da suka shafi fikira da ƙirƙira. Me ya ba ki wannan sha’awar?
Gaskiya ba zan iya ce miki ga abin da ya ba ni sha’awa ba, amma abin da na sani shi ne Allah ya ba ni baiwar da duk inda na ga wani wanda ya ke da wata fikira ko fasaha ina ganewa. Babu abin da na fi so yanzu a ce maza da matan mu musamman mata a nan Nijeriya, waɗanda suke da fasaha da basirar ƙirƙirar wani abu su ci gaba da yi don bunƙasar ƙasar mu. Kamar yadda manyan ƙasashe irinsu Chana, Indiya, Amurka suke yin abubuwan fasaha da ƙere-ƙere, wasu ma mata ne daga gidajen su kamar yadda na gani a Malesiya, yawanci su ba su dogaro da aikin gwamnati, sun fi mayar da hankalin su ga kamfanoni da wurin kasuwanci; wasu suna ƙera takalma da jakunkuna da sauran kayayyakin fasaha ga su nan iri daban-daban. To idan da ƙasarmu Nijeriya za mu yi amfani da baiwar da Allah Ya yi mana mu ɗauke ta da muhimmanci, to tabbas da yanzu mun wuce mu yi ta koke-koken rashin akin yi.

Masu karatu za su so sanin aikace-aikacen ki a matsayin mai taimakawa Gwamnan Jihar Kaduna kan fannin fikira da ƙirƙira.
Da farko dai shi mai girma Gwamna mutum ne wanda ya ke son duk abin da za a yi a kawo masa gamsasshen bayani, saboda haka sai ya sa mu zaƙulo masa mutanen da ke da fasaha da fikira a kowane irin fanni kama daga ɓangaren ma su haɗa takalma, jakunkuna, teloli, masaƙa, makaɗa da mawaƙa, ‘yan fim da masu zane-zane, masana yanar gizo, marubuta da sauran fannoni dai da dama. Sai muka fitar da fom muka rarrabawa ƙananan hukumomi 23 da muke da su a jihar Kaduna, kowace ƙaramar hukuma ta kawo irin mutanen da suke da waccan basira da fikira, duk suka cike fom ɗin da suna da adireshi da lambar waya ko da gwamnati ta na nema nan da nan babu wani ɓata lokaci za a nemi wannan mutumin da ke da wannan fasaha.

Sai abu na biyu kuma mun yi baje-kolin fasaha a shiyyoyi uku da muke da su a jihar, mun je kowace shiyya mun fito da waɗanda suka fi bada sha’awa a kan fasaharsu. Daga ƙarshe sai muka haɗa gabaɗayan su domin fitar da waɗanda suka fi birgewa da nuna tsantsan hikima da fasaha a cikin baiwar da Allah Ya yi musu. Muka kuma gayyato qwararru waɗanda suke da fasaha da basira makamanciyar irin tasu daga Legas da sauran wurare don su zo su ba su gudummuwar su da kuma ƙara nuna musu ƙwarin gwiwa. Har da abubuwan gargajiya duk an koya musu irin su raye-raye da al’adun gargajiya ta yadda muka haxa duk yaren da ke jihar Kaduna, kowanne ya zo da irin al’adun su da kalar sa suturun su da sauran su.


Bayan wannan kuma mun yi wani taro wanda kafatanin sarakunan Arewa sun halarta, dawaki kawai a wurin da aka kawo sun fi dubu biyar. Sai kuma wani taro da muka yi shi ma na baje-kolin fasaha mai taken KADAMFEST, kai mun dai yi abubuwa da dama wanda har waɗanda ke ƙasashen wajen sun shaida da irin aikace-aikacenmu na fasaha da ƙirƙira. Dalilin hakan ne ya sa shi kan shi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sai da ya jinjina mana; ya ce a rubuta wa gwamnan jihar Kaduna takardar godiya ta musamman saboda ya ga soyayya a ranar, ya ga soyayyar da bai tava gani ba a ranar saboda ɗumbin mutanen da ya zo ya gani sun taru, mutane ne ba adadi, mutane tun asubahi suna wajen, shi shugaban ƙasar bai zo ba, sai wajen ƙarfe biyu amma haka mutane suka yi tuttuɗowa kamar fari. Amma abin da gwamnati ta yi a ranar ta yi ƙoƙari saboda an raba wa mutane abinci da ruwan sha, sannan an wadata wurin da tsaro.

Haka ma ɓangaren masu shirya fina-finai su ma wannan gwamnatin na tafiya da su domin kwanan nan mai girma Gwamna ya ba su fili inda wani mai hannun jari zai gina don a samu a inganta fannin fikira; ke nan za a samu ɓangarori da masu yawa a cikin wannan gini da za a yi, fannin masu ɗaukar hoto daban, fannin daraktoci da furodusosi ko editoci da masu ɗaukar sauti da sauransu duk akwai a ciki. Kuma hakan zai sa a yi tafiyar cikin tsari ba kara zube ba.

A matsayin ki na mace wane irin ƙalubale ki ke fuskanta a wannan aikin?
Eh gaskiya a matsayi na ta ‘ya mace ko in ce ‘yar adam wanda babu wani mutum da zai ce bai taɓa fuskantar wani ƙalubale ba, kai ko a cikin gidanka ne sai ka fuskanci ƙalubale ko da kuwa kai kaɗai ne a cikinsa, haka Allah Ya halicce mu kuma dole a jarabci mutum, saboda haka duk wani abu da zan ji ko za a min na ɓatanci ko wani abu ni ban ɗauke shi ɗalubale ba, saboda abu ne da na san cewa dole ya kasance tunda Allah Ya halicci mutum, tunda a rayuwa babu yadda za a ce kowa sai ya so ka, wasu kuma za su yi maka soyayya ta tsakani ga Allah. To kin ga wannan ba wani ƙalubale ba ne, haka rayuwar take dama.

To sai dai kuma abin da zan ce mu da ma arewacin Nijeriya muna da irin wannan ɗabi’ar ta nuna gazawa ga shugabancin mace, kin ga dai duk Nijeriya wannan ofis ɗin nawa shi ne na farko. To mutanen mu na Arewa ba su saba ganin mace da irin wannan basira ba, suna tsammanin ganin namiji a wani taro da za a je kawai sai su ga mace, sai su kama mamakin ya aka yi mace ce ke wannan abu. Ba wai ina nuna kishi ba ne saboda matsayi na na mace, ni ina ganin abubuwa ba sa cika ko kuma ba sa daidaita sai an saka mata a dukkan sha’ani na rayuwar yau da kullum.

Ba wai wajen yaƙin neman zave ba, a’a mata ai su ne iyayen al’umma, ‘ya’ya namu ne, mace ita ta san ciwon ‘ya mace, uwa ita ta san halin ɗa. Ita fa mace ita ta san ciwon matasa, misali yanzu da duk abinda za a yi ana shawara da mata a sa su gaba-gaba ai abubuwa da yawa za su canja, saboda mace ita ce za ta iya kawo mafita akan wasu abubuwan da suke shige duhu. To mu a arewacin Nijeriya da yawa ma ba su amince mace ta fita ta yi aikin gwamnati ba, da yawa suna da irin wannan xabi’ar. To wannan shi ne qalunalen, to amma Alhdulillahi ni na kame kaina kuma ana ganin girmana, saboda haka ni ba irin matan nan ba ne, don na fito daga gidan girma, gidan mutumci, kuma gidan sarauta, na san tarbiyyar da suka ɗora ni akai, kuma ina da zuri’a.

Shi ya sa duk inda na je indai aka ba ni dama in yi magana, da na fara ake gane cewa wannan ba wasa ta zo yi ba, saboda ba a haxa aiki da wasa, duk abin da za ka yi ka tsaya ka yi shi tsakanin ka ga Allah. To irin wannan muke son a gyara, kuma na san akwai dubban mata irina da za su iya amfanar da al’umma a cikin wasu fannoni na rayuwa.

Hajiya, wane kalar abinci ki ka fi so?
To gaskiya ni dai ‘yar gargajiya ce, duk ban damu da cin irin abincin nan ƙyale-ƙyale ba; saboda haka ina cin waina, ina matuƙar son zogale, ina son fankasau, ina cin ɗanwake, ina shan kunu da ƙosai, sai kuma irin su tuwon madara da aya da sauransu.

Mene ne sirrin kwalliyar ki kasancewar a kowane taro na hango ki sai in ga kwalliyarki ta disashe ta sauran mata?
Gaskiya ban san me ya sa mutane suke kallon kwalliyata ba, ni dai abin da na sani shi ne ba na sa irin abin da wasu suke sa wa, misali ni dai ba na yin abubuwan ya yi, sannan ba na kwaikwayon wani, na fi son duk abin da zan sa daga zuciyata ne. To amma zan iya cewa gyaran jiki da gyaran gida kamar wani abu ne da na koya kuma ya zame min jiki; shi ya sa duk wanda ya je gidana ya san gidana ne, to haka ma nake yin kwalliyata fes wanda ni ne na yi abu na ba wai wata ƙwararriya ba, shi ya sa da wahala ki ga wata da irin abin da na saka. Sannan duk kayan da zan ɗinka idan atamfa ce ni nake bada kalar irin wanda nake so. Gaskiya dai a taƙaice ba na son abin da ake yayinsa.

Me ya fi burge ki?
Gaskiya ina son in ga mutum mai basira wanda ya san abinda yake yi, wanda da na fara magana da shi zan fahimci cewa ya san abin da ya ke yi, ya na da ilimi. Kuma a duniyar nan babu abin da nake so illa in ga ina karanta littafi, ina son karatu sosai. Ina son tattaunawa da mutum, kuma ina son mutum mai gaskiya da riƙon amana, ba na son maƙaryaci. To abubuwan da ke birgeni dai gaskiya suna da yawa, ina son furanni, ina son shan ganyen shayi. Ina son motoci haɗaɗɗu masu kyau, amma ba na son wadda mutane da yawa suna da ita, kowa yana yayinta.

Me ke saurin ɓata miki rai?
Gaskiya ba na son raini, ƙarya, rashin yarda, cin fuska da munafunci; duk ba na son su suna ɓata min rai matuƙa.