Gwamnati ta amince da shirin kula da dattawa, inji Minista Sadiya

Daga WAKILIN MU

Majalisar Gudanarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da sabon Shirin Kula Da Masu Manyan Shekaru ta Ƙasa, a turance ‘National Policy on Aging’, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tabbatar da tsaron lafiya da tattalin arzikin mutanen da yawan shekaru ya cim masu.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Laraba, jim kaɗan bayan taron hukumar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar ta, manufar shirin ita ce domin a tabbatar da cewa dattijai sun samu kariya, tsaro, damar shiga a dama da su da kuma cikakkiyar kula tare da samun cikar buri da gamsuwa.

Ta ce, “Shirin ya haɗo ɗimbin al’amura da damarmaki saboda dattawa, da dattawa masu wata naƙasa, da dattawa ‘yan gudun hijira, da dattawa da ke noma a yankunan birane da karkara a Nijeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *