15
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna jirgin saman da ke ɗauke da allurar rigakafin annobar cutar korona wadda ƙasar Sin ta bayar gudunmawa ga ƙasar ya isa filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Robert Mugabe da ke Harare, babban birnin kasar, da asubahin wannan Litinin. Da yake jawabi a filin jirgin, Mataimakin Shugaban Ƙasar Zimbabwe Constantino Chiwenga, ya ce ƙasar Sin ta jima tana taimaka wa Zimbabwe kan sha'anin yaƙi da annobar korona, kuma gudunmawar rigakafin zai taimaka wa ƙasar a yaƙin da take yi da annobar. Kazalika, Chiwenga ya ce gudunmawar za ta yi tasiri…
