18
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA A ranar Asabar mai zuwa, 20 ga Fabrairu, 2021, za a ƙaddamar da wani littafi da aka wallafa a kan salatin Annabi Muhammadu (SAW) a Kano. Littafin, mai taken 'Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam: Matsayinsa Da Fa'idojinsa Da Sigoginsa', wata marubuciya mai suna Hajiya Hajara Muhammad Kabir ce ta wallafa shi. Ɗan kwamitin yaɗa labarai na shirya taron, Malam Ibrahim Sheme, ya bayyana cewa za a ƙaddamar da shi ne a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da ƙarfe 10 na safe. A cikin takardar sanarwa ga manema labarai, Sheme ya ce manyan baƙi daga sassa…
