Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO

Daga AISHA ASAS

Majalisar Ƙoli ta Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), ta tabbatar da Dr. Ngozi Okonjo-Iweala daga Nijeriya a matsayin Babbar Daraktar ƙungiyar.

Da wannan, Okonjo-Iweala ta zama ta bakwai kenan daga jerin waɗanda suka riƙe wannan muƙami.

Ranar 1 ga watan Maris ake sa ran Okonjo-Iweala za ta kama aiki, inda za ta kasance mace ta farko daga Nahiyar Afirka da ta taɓa ɗarewa kan muƙamin.

Za ta riƙe wannan muƙami ne na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, wato dai wa’adinta zai ƙare ne ya zuwa 31 ga Agustan 2025.

A cewar Shugaban Majalisar ƙungiyar, David Walker daga New Zealand, “Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga WTO. A madadin majalisar, ina taya Dr Ngozi Okonjo-Iweala murnar naɗin da aka yi mata a matsayin Babbar Daraktar WTO.”

A nata ɓangaren, Okonjo-Iweala ta nuna amincewarta da naɗin da aka yi mata. Tare da nuna godiyarta ga dukkan waɗanda suka mara mata baya yayin neman matsayin. Kana ta yi alƙawarin yin aiki da gaskiya don cigaban WTO.