Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Daga WAKILIN MU

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana farin cikin sa kan yadda aka raba kuɗi naira miliyan tamanin ga matan jihar su 4,000 a ƙarƙashin shirin tallafa wa matan karkara da jari wanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.

Gwamnan ya faɗi haka ne lokacin da Ministar Harkokin Jinƙai Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta kai ziyara a jihar a ranar Asabar.

Gwamnan ya ce shirin na ‘Cash Grant for Rural Women’ zai taimaka wa matan jihar da dama wajen ficewa daga ƙangin fatara da yunwa.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matabele Alli, ya wakilta, ya ce tallafin ya zo ne a daidai lokacin da jama’ar Jihar Neja su ke fama da fatara sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu ba ƙaƙƙautawa wanda hakan ya sanya da yawan su sun koma sansanin ‘yan gudun hijira da zama, da satar shanu da kuma annobar korona da ta zo a watannin baya.

Ya ce ya tabbatar matan za su yi amfani da tallafin wajen inganta rayuwar su.

Ya ce, “Na gode wa mai girma Shugaban Ƙasa da ya kawo wannan tsari na taimakon matan karkara a duk faɗin ƙasar nan ta hanyar wannan Tallafi na Musamman.

“Mu na godiya kan dukkan tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya da aka ba wannan jiha saboda ambaliya, hare-haren ‘yan bindiga, shirin ‘Conditional Cash Transfer’, ‘GEEP’, ‘N-Power’ da kuma ‘Home Grown School Feeding Programme’ da sauran su.

“Har yanzu mu na buƙatar ƙarin taimako a Jihar Neja. Mutanen mu sun ƙara shiga cikin matsin fatara saboda yanayin rashin tsaro da ‘yan bindiga su ka janyo, da satar shanu da sauran matsalolin rayuwa.

“Duk da haka, ina tabbatar maku da cewa waɗannan matan za su yi matuƙar amfani da wannan tallafin kuɗin da aka ba su.”

Tun da farko a wajen ƙaddamar da shirin a jihar, sai da Minista Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa shirin bada kuɗin tallafin wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto faƙirai daga tarkon fatara.

Ta ce, “Ran ka ya daɗe, a matsayin wani sashe na yunƙurin Gwamnatin Tarayya na kawar da fatara da yunwa a faɗin ƙasar nan, an fito da babban Shirin Agajin Jama’a na Ƙasa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP) da zai inganta rayuwar waɗanda su ka fi kowa talauci a ƙasar nan kuma ya na daga cikin manyan tsare-tsaren yaƙi da talauci a Afrika.

“A matsayin wani ɓangare na tsinkayar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara cikin shekaru 10, Gwamnatin Tarayya ta hanyar ma’aikata ta ta shigo da Shirin Bada Tallafin Kuɗi ga Matan Karkara wanda mu ke ƙaddamarwa a yau. An tsara shi ne ta yadda za a yi biyan kuɗi N20,000 sau ɗaya ga matan da su ka fi kowa kasancewa cikin fatara a yankunan karkara a Nijeriya don sama masu hanyar karɓar kuɗin da za su ja jari domin su fara sana’a.

“Ana raba kuɗin ne ga matan karkara su sama da 150,000 a duk faɗin jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.”

Da ma can ita Jihar Neja an riga an ba ta jimillar kuɗi N1,991,070,000.00 (naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari tara da casa’in da ɗaya da dubu saba’in) daga shirin Gwamnatin Tarayya na Tallafin Tiransifar Tsabar Kuɗi, wato ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT), wanda ya shafi rayuwar gidajen mabuƙata guda 43,611 (PVHHs).

Ƙananan hukumomi 12 da su ka haɗa da Wushishi, Chanchaga, Bida, Kontagora, Rafi, Bargu, Agaie, Mashegu Katcha, Bosso, Munya, Lapai, da Lavun a yanzu duk su na amfana da wannan shirin Gwamnatin Tarayya na CCT a Jihar Neja.

An zaɓo masu cin moriyar shirin bada tallafin kuɗi ga matan karkara ne daga ƙananan hukumomi 25 na jihar.

Manyan baƙi a wajen taron ƙaddamarwar sun haɗa da ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Ambasada Zubair Dada, da Darakta Janar na hukumar NEMA, AVM Muhammadu Alhaji Muhammed, da Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, Alhaji Muhammed Abdullahi Bawa Wuse wanda shugabar Kwamitin Mata na majalisar, Hajiya Binta Mamman ta wakilta, da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Neja, Hajiya Salamatu T. Abubakar, da Daraktan Kuɗi da Gudanarwa mai kula da NSIP a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Malam Abdullahi Musa Yusuf, da jami’ar kula da shirin tallafi a Jihar Neja kuma mai bada shawara na musamman kan shirye-shiryen agaji, Barista Amina Musa Gu’ar, da Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Neja, Hajiya Tasalla Fati Ibrahim, da sauran jagororin mata.