Kwamiti ya yi zaman farko don magance rashin zuwan yara makaranta

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kwamitin Gudanarwa kan Shirin Sabuwar Hanyar Bada Karatu (National Steering Committee on Alternate School Programme) ya yi taron sa na farko a ranar Litinin a Gidan Ma’aji (Treasury House) da ke Abuja.

Taron ya fara aiwatar da tsare-tsare kan hanyoyin da za a bi a magance matsalolin da ke sanya yara su daina zuwa makaranta a Nijeriya tare da gaggauta rage yawan irin waɗannan yaran ta hanyar sama masu ilimin farko mai inganci da ilimin sana’o’in a wasu yanayi na musamman waɗanda ba a magance su a tsarin da ake da shi a yanzu ba.

A jawabin ta na buɗe taron, ɗaya daga cikin shugabanni biyu na kwamitin, kuma wadda ta kira taron, Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa Nijeriya ce a sahun gaba na ƙasashen da ke da yaran da ba su zuwa makaranta a duniya, wanda hakan ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta fito da dabarun musamman ta hanyar ƙaddamar da wannan Kwamitin Gudanarwan kwanan nan.

Ta ce: “Sanin ku ne cewa Nijeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa a duniya wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta. Saboda haka ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta (ASP) domin tabbatar da cewa kowane yaro da bai zuwa makaranta a Nijeriya ya samu hanyar samun ingantaccen ilimin farko, ba tare da nuna masa bambancin wajen zama, al’ada ko matsayin tattalin arziki ba.

“Ana sa ran cewa Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta zai taimaka wajen samar da damammaki ga yaran da ba su zuwa makaranta don su samu ƙwarewar da za ta tallafi rayuwar su daga koyarwar sana’o’i da kasuwanci da za a yi masu domin su amfani al’umma.

“Kowanne daga cikin membobin wannan Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa an zaɓe shi ne cikin tsanaki a cikin tunanin ɗimbin gudunmawar da zai kawo wajen fito da hanya mafi dacewa da za a bi a wannan shiri.”

An tsara Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta ne don ya inganta hanyar da za a samar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nijeriya kamar yadda Shirin Kyautata Rayuwa (SDG-4) ya tanada kan samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa kuma ya rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta ƙwarai da gaske ta hanyar gwama tsarin karatun aji da wanda ba na shiga aji ba.

Manufar sa ita ce ya kawar da ko kuma ya rage yawon banza matuƙa, barace-barace na ƙananan yara, sannan ya haɓaka zaman lumana, haɗin kai da tattaro yara wuri guda daga sassan rayuwa daban-daban.

Ayyukan da aka ba ‘yan kwamitin sun haɗa da tabbatar da tsare-tsaren shirin na ASP sun fara aiki sosai a duk faɗin ƙasar nan, su ƙara goge tare da tsara manufar shirin, su duba kowane aiki tare da amincewa da shi, kuma su aiwatar da tsare-tsare tare da yin duk wani aiki da zai inganta aiwatar da shirin.

Kwamitin mai membobi 17 ya na ƙarƙashin shugabancin Minista Sadiya da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu.

Sauran ‘yan kwamitin su ne Ƙaramin Ministan Ilimi, da Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan SDGs, da Ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, da Babban Sakataren Hukumar Bada Ilimin Farko (UBEC), da kuma wakilan (UNESCO) da (UNICEF) da ‘Global Partnership for Education’.

Sauran su ne shugaban ƙungiyar mashawarta kan sana’o’i masu zaman kan su (SDGs) da shugaban haɗakar mashawarta masu zaman kan su kan cigaban ƙasa, da shugaban Kwamitin Ilimin Farko a Majalisar Dattawa, da shugaban Kwamitin Ilimin Farko a Majalisar Wakilai, Hon. Dr. Shehu Balarabe Kakale, da Darakta Janar na NYSC, da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa Bashir Nura Alƙali a matsayin Sakatare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *