Editor

9513 Posts
Samar da ilimi da cigaban rayuwa: Yadda Abdulnaseer Bobboji ya taka rawar gani a Jalingo

Samar da ilimi da cigaban rayuwa: Yadda Abdulnaseer Bobboji ya taka rawar gani a Jalingo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Jalingo A rayuwar duniya ta wannan lokaci, babu wani abu da a ke buƙatar ɗan Adam ya samu kamar ilimi na zamani da kuma na addini. Wannan ya sa ƙasashen da suka cigaba sika ɗauki ɓangaren ilimi da muhimancin gaske ta yadda su ke ba shi kyakyawar kulawar da ta dace, domin kuwa ana samun al'umma masu cigaba ta hanyar bunƙasar iliminsu ta kowanne ɓangare. Domin masana sun ce babu wata al'umma da za ta ci gaba tana cikin duhun jahilci, don haka ne duk wata gwamnati walau ta tarayya ko ta ƙaramar hukuma da ta…
Read More
Gumi ya shiga tsakani don neman kuɓutar da ɗaliban Kagara da aka sace

Gumi ya shiga tsakani don neman kuɓutar da ɗaliban Kagara da aka sace

Daga AISHA ASAS Alamu da dama kuma masu gamsarwa sun nuna fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmed Gumi, ya shiga tsakani domin kuɓutar da ɗaliban nan su 27 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kagara, Jihar Neja, cikin wannan makon. Bayanai daga jihar Neja sun tabbatar da Sheikh Gumi ya ziyarci Neja ya samu ganawa da 'yan bindigar da suka kwashe ɗaliban a dajin Bangi a ranar Alhamis. Idan da dai za a iya tunawa, a daren Larabar da ta gabata 'yan bindigar suka kai hari a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a yankin ƙaramar…
Read More
Zamfara: Wani jigon APC ya musanta zancen yana da matsala da EFCC

Zamfara: Wani jigon APC ya musanta zancen yana da matsala da EFCC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani  mai ruwa da tsaki kuma tsohon ɗan takarar gwamna a Zamfara yayin zaɓen 2019, Hon. Aminu Sani Jaji ya ce bai san da wata shari’a da ta haɗa shi da hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ba har ta kai ga sanya masa alama a gidansa da ke Gusau ranar Juma’a. Ɗan siyasar wanda ya yi magana da ’yan jaridu a wayar tarho ya ce, babu wanda ya gayyace shi ko ya kusanta shi ko dai a EFCC ko kuma a ko wace hukuma, kuma saboda haka ya zama abin mamaki a gare…
Read More
Masu Umura daga Nijeriya sun isa Saudiya

Masu Umura daga Nijeriya sun isa Saudiya

Daga WAKILIN MU An samu ƙarin 'yan Nijeriya su 23 suka bar gida zuwa ƙasa mai tsarki a Alhamis da ta gabata domin gabatar da aikin Umura. Maniyatan sun tashi ne ta babban filin jirgin saman Murtala da ke Legas zuwa babban filin jiragin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah. Saudi Arabia. HAJJ REPOTERS ta ruwaito cewa kamfanonin New Crescent International Travels da kuma Rhoudah Travel sun taimaka wajen tsara tafiyar maniyatan zuwa ƙasa mai tsarki. Ethiopian airline mai lamba ET 2402 shi ne jirgin da ya yi jigilar maniyatan inda suka isa Saudiya bayan shafe sa'o'i biyar a…
Read More
Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya, Abdullahi Dikko Inde, rasuwa a ranar Alhamis (18/02/2021). Iyalan marigayin ne suka bada bayanin tabbacin rasuwarsa. Sanarwar da ta fito daga hannun Mai Magana da Yawun Hukumar Kwastam na Ƙasa, DC Joseph Attah, ta nuna za a gudanar da jana'izar marigayin a ranar Juma'a (19/02/2021), bayan sallar Juma'a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja. A halin rayuwarsa, marigayin ya shugabanci Hukumar Kwastam daga 2009 zuwa 2015. Attah ya yi fatan Allah Ya bai wa iyalan marigayin danganar wannan rashi, tare da fatan Allah Ya sa Aljanna ta…
Read More
Neja: Jerin sunayen waɗanda ‘yan bindiga suka sace a Kwalejin Kimiyya, Kagara

Neja: Jerin sunayen waɗanda ‘yan bindiga suka sace a Kwalejin Kimiyya, Kagara

Daga BASHIR ISAH A ranar 17/02/2021 wasu 'yan bindiga suka kai hari a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a yankin ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai da sauransu. Manhaja ta yi ƙokarin tattaro sunayen waɗanda lamarin ya shafa, ga su kamar haka: Malamai da ma'aikata da sauransu; Hannatu PhilipLawal AbdullahiDodo FodioMohammed MusaFaiza MohammedChristiana AdamaFaith AdamaMaimuna SuleimanNura IsahAhmad IsahKhadizat IsahMohammed MohammedAisha IsahSaratu Isah . Ɗalibai; Jamilu IsahShem JoshuaAbbas AbdullahiIsah AbdullahiEzekeil DanladiHaliru ShuaibuMamuda SuleimanDanzakar DaudaAbdulsamad SanusiBashir AbbasSuleman LawalAbdullahi AdamuHabakuk AugustineIdris MohammedMusa AdamuAbdulkarim AbdulrahmanAbubakar DanjummaAbdullahi AbubakarBashir KamalideenMohammed SalisuYusuf M KabirIsah Abdullah MakusidiPolineous VicenteLawal…
Read More
NAFDAC ta gamsu da ingancin rigakafin AstraZeneca

NAFDAC ta gamsu da ingancin rigakafin AstraZeneca

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ce, ta amince da ingancin maganin rigakafin korona na AstraZeneca don amfanin ƙasa. Shugabar hukumar, Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a wannan Alhamis. Da wannan, Nijeriya ta samu shiga jerin ƙasashen duniya da ke da dama wajen yaƙi da annobar korona. Yayin da take yi wa taron manema labarai bayani a Abuja, Adeyeye ta ce bayan da hukumar NAFDAC ta karɓi maganin, ba tare da ɓata lokaci ba ta sukunya bincike don tabbatar da ingancinsa. A cewar Adeyeye, baya ga rigakafin AstraZeneca da ta…
Read More
Majalisa ta buƙaci Buhari ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaro

Majalisa ta buƙaci Buhari ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaro

Daga WAKILIN MU Majalisar dattijan Najeriya ta buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaron da suka addabi sassan Nijeriya. Majalisar ta buƙaci haka ne bayan da ‘yan bindiga suka sace ɗalibai sama da 20 a Kwalejin Kimiyya ta Kagara, Jihar Nejs'a, a Larabar da ta gabata. Sanata Sani Musa da ke wakiltar gabashin Jihar Neja, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin neman shelar dokar ta-ɓacin, ya ce ‘yan bindigar da suka sace ɗaliban na sanye ne da kayan sojoji. Haka nan, Majalisar ta bumaci hukumomin tsaron Nijeriya da su kafa rundunar haɗin gwiwa sojoji…
Read More
NAFDAC ta garƙame masana’antu 13 a Kano

NAFDAC ta garƙame masana’antu 13 a Kano

Daga AISHA ASAS Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ce ta garƙame wasu masana'antun sarrafa madara a jihar Kano saboda rashin yin rijista da hukumar. Kodinetan NAFDAC a Kano, Alhaji Shaba Mohammad ne ya shaida wa manema labarai haka jim kaɗan bayan kammala aikin rufe masana'antun a ranar Alhamis. Jami'in ya ce hukumar ta dukufa aiki wajen ganin ta bankaɗo masu yin jabun kayayyaki suna saida wa jama'a domin kare lafiyar al'umma. Ya ci gaba da cewa, bayan sun bincika sun gano waɗannan wurare na sarrafa abubuwa mara inganci sai suka sunkuya aiki inda suka…
Read More
Kwastam ta kama kayayyakin da harajinsu ya haura milyan N74 a shiyyar Kaduna

Kwastam ta kama kayayyakin da harajinsu ya haura milyan N74 a shiyyar Kaduna

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a shiyyar 'Zone B' mai hedikwata a Kaduna ƙarƙashin jagorancin Comptroller AB Hamisu, ta samu nasarar kama kayyakin da aka yi fasa-ƙwaurinsu wanda harajinsu ya haura Naira miliyan 74. Bayanan hukumar sun nuna wannan kamen da hukumar ta yi ya faru ne cikin Fabrairun da ake ciki, ciki har da gano ɗaruruwan buhun shinkafar ƙetare da aka ɓoye a rumbunan ajiya daban-daban sassan shiyyar. A cikin takardar sanarwa ga manema labarai da ta fito ta hannun Mai Magana da yawun hukumar na shiyyar Zone B, ASC1 MA Magaji, Hamisu ya lissafo…
Read More