NAFDAC ta gamsu da ingancin rigakafin AstraZeneca

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ce, ta amince da ingancin maganin rigakafin korona na AstraZeneca don amfanin ƙasa.

Shugabar hukumar, Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a wannan Alhamis.

Da wannan, Nijeriya ta samu shiga jerin ƙasashen duniya da ke da dama wajen yaƙi da annobar korona.

Yayin da take yi wa taron manema labarai bayani a Abuja, Adeyeye ta ce bayan da hukumar NAFDAC ta karɓi maganin, ba tare da ɓata lokaci ba ta sukunya bincike don tabbatar da ingancinsa.

A cewar Adeyeye, baya ga rigakafin AstraZeneca da ta tantance akwai wasu ƙarin magani guda uku da take kan gudanar da aikin tantance su.

Ta ci gaba da cewa, bincikensu ya gano maganin AstraZeneca zai iya yaƙi da ƙwayar cutar korona irin wadda ta ɓulla a Ingila da kuma wadda aka sani a Nijeriya.

Ta jaddada cewa nau’in korona da ta ɓulla a Afirka ta Kudu ba a ga irin ta ba tukuna a Nijeriya. Tana mai cewa, yanzu haka akwai magungunan gargajiya sama da 30 da hukumar ke nazarin su.