Kamfanin BUA ya samu ribar bilyan N95 a 2020

Daga AISHA ASAS

Kamfanin sarrafa siminti na BUA, ya bada sanarwar cewa ya tara kuɗaɗen shiga har naira bilyan N209 a 2020 inda ya ce ya samu ƙarin kashi 19 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da ya tara 2019.

Haka nan, kamfanin ya ce a bara ya samu ribar naira bilyan N95.4 wanda a cewarsa hakan ya ɗara ribar da ya samu a 2019 da kashi 16 cikin 100 inda ya samu naira bilyan N82.4.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun Shugaban Sashen Sadarwa na Kamfanin, Sunday Ogieva, wadda Manhaja ta samu kwafinta.

Sanarwar ta nuna cewa da wannan nasarar da kamfanin ya samu, hakan ya sanya kamfanin ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin Nijeriya da ke kan gaba wajen samun riba mai tsoka.

A cewar kamfanin, samun wannan nasarar zai ƙarfafa masa wajen ƙaddamar da reshensa a Sakkwato a bana, da kuma bunƙasa ayyukansa a Adamawa da Edo da Sakkwato ya zuwa 2023 inda ya ce har ma sun sanya wa wata yarjejeniya hannu tare da kamfanin Sinoma CBMI.

Sanarwa ta nuna bayan kammala komai, ana sa ran kamfanin BUA ya riƙa samar da siminti mai yawan metrik tan milya 20 a cikin shekara. A halin yanzu dai BUA shi ne kamfani mafi girma na biyu a Nijeriya da yake samar da siminti.