Daga WAKILIN MU
Dan wasan damben nan Kamaru Usman, wanda ɗan asalin Nijeriya ne, ya sake lashe kambunsa na UFC bayan da ya doke Gilbert Burns daga ƙasar Brazil a karawar da suka yi a Lahadin da ta gabata.
Wannan shi ne karo na uku da Usman ke samun nasarar lashe wannan kambu.
Ya samu nasarar farko ne a 2019 bayan da ya doke Colby Covington, sai ta biyu da ya samu a 2020 bayan da ya doke Jorge Masvidal.
Yayin wasan baya-bayan nan, Usman bai yi wa Burns da wasa ba inda ya bambance masa tsakanin aya da tsakuwa.
Burns ya yi ƙoƙarin maida martani amma Usman bai ba shi zarafin haka ba.