‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 21 a Neja

Daga AISHA ASAS

Masu satar mutane a jihar Neja sun kama mota (bas) sukutum mallakar gwamnatin Neja (NSTA) ɗauke da fasinjoji 21 a daidai ƙauyen Yakila a cikin ƙaramar hukumar Rafi.

Bayanan da Manhaja ta samu, sun nuna motar ta fito ne daga garin Kontagora zuwa Minna, babban birnin jihar, inda ɓarayin suka tare ta a hanya.

Sannan fasinjoji 21 da ke cikin motar, ɓarayin sun tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji, suna yi suna harbin bindiga a iska, lamarin da ya razana mazauna ƙauyen inda kowa ya yi gudun neman mafaka.

Bayanai sun nuna yankin Yakila ya zama tamkar maɓuyar ‘yan ta’addan inda suke ɓuya suna addabar mutane. Ko a kwanakin baya, sun yi garkuwa da wani basarake a yankin wanda daga bisani suka kashe shi.

Shaidu sun ce an ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Neja, Ibrahim Balarebe ya hallara wurin da lamarin ya faru jim kaɗan bayan aukuwarsa yayin da yake dawowa daga Kagara, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Rafi.

Daraktan Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar, Malam Ibrahim Inga, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai duk ƙokarin neman jin ta bakin Mai Magana da Yawun ‘yan Sandan Jihar, Wasiu Abiodun, kan batun ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *