Daga WAKILIN MU
An bayyana cewa ‘yan fashin daji da ke dazuzzakan jihohin Arewa suna shirin mallakar makaman kakkaɓo jirgin yaƙi domin daƙile hare-haren sojoji. Sheikh Abubakar Gumi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da jaridar PUNCH ta yi da shi.
A kwanankin baya ne Gumi ya ziyarci ‘yan ta’addar a dajin Zamfara ya gana da su inda suka nuna suna satar mutane suna karɓar fansa ne domin tara kuɗaɗen sayen makamai.
Bayan dawowarsa, Gumi ya yi kira ga gwamnati da ta duba ta yi wa ɓarayin afuwa domin ba su damar ajiye makamansu.
Yayin ziyarar tasa Gumi ya ce ya fahimci ɓarayin sun shiga harkar sace-sacen mutane ne don ɗaukar fansa kan kashe musu iyalai da ɓarayin shanu suka yi da kuma hare-haren sojoji.
A cewarsa ɓarayin suna neman a bi musu kadin cutar da su da aka yi. Sannan ya nuna akwai buƙatar gwamnati ta hanzarta ganawa da waɗannan mutane tun kafin lokaci ya ƙure su rikiɗe su zama kamar mayaƙan Boko Haram.
Ya ce, “Waɗannan mutane ne da ɓarayi suka raba su da dabbobinsu saboda ɓarayin suna amfani da bindigogi. Ganin cewa sun rasa shanunsu ya sa su ma suka haɗu da ɓarayin suka soma sace-sacen mutane.
“Gaskiyar ita ce, galibin sace-sacen mutane da suka yi, sun yi haka ne domin samun kuɗin sayen makamai. Yanzu ƙoƙari suke yi su mallaki makamai masu linzami na kakkaɓo jiragen yaƙi.
“Al’amrin ya kama hanyar zama cikakken ta’addanci, ya kamata mu daƙile shi. Abin da muke tsoro shi ne, kada matsalar ta rikiɗe ta zama ta mayaƙan addini ta yadda ba za a iya magance ta ba. Kalli abin da Boko Haram ta zama mana.”
Saɓanin abin da wasu ke tunani, malamin ya ce akwai yiwuwar ɓarayin ba sa samun kowane tallafi daga hannun ‘yan siyasa ko haɗin gwiwa da wasu daga ƙetare.
Yana mai cewa suna mallakar muggan makamai ne ta hanyar kuɗaɗen fansar da suke karɓa sakamakon sace-sacen mutane da suke yi. Amma ba wai tallafi suke samu daga wajen ‘yan siyasa ko makamantansu ba.
“Kamar yadda na faɗa a baya, waɗannan mutane suna karɓar kuɗaɗen fansa ne ba don komai ba sai don sayen makamai. Dubi makiyaya a jihar Oyo da sauran jihohin kudancin ƙasa, har yanzu a dazuzzuka suke zama. Dabbobinsu kawai suke buƙata amma ba kuɗaɗe ba. Suna harkar (satar mutane) ne don kawai su samu halin mallakar makamai da za su yi amfani da su wajen daƙile hare-haren sojoji da na duk wanda ya yi nufin kawo musu hari.
“Ya kamata ku fahimci tunanin waɗannan mutane, ba kamar gwamnoninmu suke ba ma su wawushe dukiyoyinmu. Su a gare su, dabbobinsu sun fi kuɗi daraja.”
Sai dai, Gumi ya ce ya fahimci akwai wasu daga cikin sojoji da ke aiki tare da su.
Inda ya ce, “Suna da waɗanda suke aiki tare a ko’ina, akwai su a sojoji, akwai su a ko’ina. Ɗaya daga cikinsu ya faɗi cewa, ‘Hatta shanun da muke sacewa ba mu da manyan motocin da za mu yi jigilarsu zuwa mayanka. Ba mu da kwata. ‘Don haka wannan ya nuna akwai wasu da suke aiki tare. Ko satar mutane da suke yi, sun ce, ‘Mu ba mu san waɗannan mutanen ba, ‘yan gari ne ke tsegunta mana masu hali daga cikinsu.
Malamin ya yi gargaɗin cewa muddin gwamnati ta gaza ɗaukar matakin da ya dace a yanzu, matsalar satar mutane za ta yaɗu daga Arewa inda ta fi ƙamari zuwa Kudu. Yana mai ra’ayin cewa hanyar da ta fi dacewa a yi amfani da ita wajen magance matsalar shi ne tattaunawa da waɗanda lamarin ya shafa da kuma yi musu afuwa, maimakon yin amfani da ƙarfin soji.
A cewarsa, “Mutanen sun san yadda suke shiyarwa da kuma bai wa kawunansu kariya, ga shi kuma sun soma bin ƙauyuka suna kai hare-hare. Muddin ka taɓa ɗayansu, haka za su haɗa kansu su kai harin ɗaukar fansa. Don haka haɗari ne a kai musu hari. Kuma mutane ne masu kunya sosai.”
Ya yi kira ga gwamnati da ta nemi waɗannan mutane ta yi zama da su, ta yi musu afuwa sannan ta dawo da su cikin al’umma don ci gaba da rayuwa ta hanyar gina musu makarantu da asibitoci. A yi ma kowannensu rajista ta haka za a iya tafiyar da su.
“Mutane ne da ba za a iya shawo kansu da ƙarfin bindiga ba. Gaskiyar ita ce, sun fi sojojinmu sanin dajin da suke zaune a ciki. Don haka mafi alheri shi ne a yi zaman tattauna da su.”
Sai dai kiran da Gumi ya yi bai samu karɓuwa ba a wajen galibin jama’a kuma ya sha suka daga sassan ƙasa.