Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Kamfanin shirya finafinai na M. Soja Concept NIG. LTD yana cigaba da ɗaukar sabon fim ɗin barkwanci mai dogon zango mai suna ‘Jikokin Mai Gari’.
Fim ɗin wanda yanzu haka ake ɗaukarsa a guraren daban-daban a Jihar Kano, ana sa ran fitowarsa nan ba da daɗewa ba.
Mujahid M. Soja wanda shi ne daraktan fim ɗin kuma shi ne ya ƙirƙiro labarin, ya bayyana cewa an gina labarin ne don nishaɗartarwa da faɗakarwa iri-iri.
“Jikokin Mai Gari’ fim ne da aka gina shi akan wasu yara biyu da suka kasance jikoki ga mai garin garin, inda suka addabi kowa a garin, ta yadda suka fitine mutan gari, kuma fitinar ta su ta samo asali ne saboda wani buri da suke so su cimma, kuma dukka suna yi ne saboda mai gari ya gaji da su ya kore su,” Inji Mujahid M. Soja.
Kamilu Ibrahim Ɗan Hausa shi ne furodusa na fim ɗin ya bayyana cewa an yi ƙoƙari wajen sanya jarumai da za su ja hankali tun daga kan yara da matasa da kuma tsofaffi da za su ja hankalin ‘yan kallo.
Ɗan Hausa ya ƙara da cewa, “Fim ne da zai faɗakar ya nishaɗantar da al’umma domin an yi shiri na musamman.”
Fim ɗin da ake ɗaukar sa a ARTV da garin Langel, fitattun jarumai da dama sun taka rawa a ciki kamar A’isha Najamu, Sulaiman Botsho da Billisu Be Safana da Adam M. Adam da Samira Sani da sauran jarumai maza da mata.
