Zargin cushen kasafi: Majalisa ta yi wa Sanata Abdul Ningi afuwa

Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata Abdul Ahmed Ningi afuwa tare da kiran sa ya koma bakin aiki bayan da ta dakatar da shi a ranar 12 ga watan Maris, 2024.

A ranar Talata Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Sanata Abba Moro, ya gabatar da buƙata dawo da Ningi tare da yin dama a madadin Ningin kan abin da ya faru.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, shi ne ya ba da sanarwar dawo da Ningi bakin aiki bayan da wasu daga cikin sanatotcin suka ruƙi a yi masa afuwa.

Afuwar na zuwa ne makonni biyu kafin ƙarewar wa’din dakatarwa na wata ukun da aka yi masa, wanda zai cika ya zuwa ranar 12 ga watan Yuni, 2024.

Ningi ya fuskanci dakatarwa ne bayan da ya yi zargin cewar, an tafka cushe har na Naira tiriliyan 3.7 a kasafin 2024.