28
Sep
Erling Haaland ya zura ƙwallo na 100 a raga a Manchester City ranar Lahadi a wasan da suka yi 2-2 da Arsenal a Firimiyar Ingila. Shi ne ya fara cin Arsenal a karawar ta hamayya a Etihad, kuma na 10 a kakar nan, sh ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a bana da fara babbar gasar tamaula ta Ingila. Dan wasan tawagar Norway ya ci na 100 a City a karawa ta 105 a kaka biyu tun bayan da ya koma Etihad daga Borussia Dortmund. Haaland na taka rawar gani a bana a Premier League da 10 a raga…