A Amurka Iran za ta buga Gasar Kofin Duniya duk da rikicin Gabas ta Tsakiya – Infantino

Spread the love

Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya tabbatar da cewa, tawagar ƙasar Iran za ta halarci Gasar Kofin Duniya ta 2026 a ƙasar Amurka kamar yadda aka tsara tun farko, duk kuwa da ƙalubalen siyasa da tsaro da ke ƙara ta’azzara a duniya.

A wata hira da ya yi da tashar N+ Univision, wadda kamfanin dillancin labarai na Jamus (dpa) ya rawaito, Infantino ya ce babu wani shiri na madadin da FIFA ke da shi dangane da tsarin gasar, yana mai jaddada cewa shirin farko kaɗai ake da shi.

“Mu na rayuwa a cikin gaskiya, kuma mun san irin rikitarwar da ke tattare da halin da tawagar Iran ke ciki. Amma muna aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa sun buga wasanninsu cikin yanayi mafi kyau. Babu wani tsari na B ko C ko D — akwai tsari A kaɗai,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, duk da irin mawuyacin yanayin siyasa na duniya, wasanni na da rawar da za su taka wajen haɗa kan al’umma da samar da yanayi na zaman lafiya da murna.

Wannan bayani ya biyo bayan buƙatar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran ta gabatar, inda ta nemi a mayar da wasannin rukuni daga Amurka zuwa Meɗico saboda matsalolin tsaro.

By ukarofi