Yayin da ake ci gaba da ƙara ƙidayar lokaci zuwa gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026, hankalin duniya ya karkata ga babbar kyauta mafi daraja a harkar ƙwallon ƙaf, wato kofin zinariya na FIFA.
Daga ranar 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli, ƙasashen Amurka, Kanada da Meɗico ne za su karɓi baƙuncin wannan gagarumar gasa mafi girma a tarihi, inda za a fafata da ƙungiyoyi 48 a karon farko. Za a buga wasanni 64 a birane 16, tare da wasan ƙarshe da zai gudana a MetLife Stadium.
A yayin da fitattun ’yan wasa ke shirin fafatawa domin lashe wannan kofi mai daraja, hukumar FIFA ta fitar da wasu bayanai masu ban sha’awa game da kofin. Ga wasu muhimman bayanai guda shida da kowane mai sha’awar ƙwallo ya kamata ya sani:
Kofin ya fi nauyi fiye da yadda ake tsammani. Duk da kamanninsa masu jan hankali, kofin yana da nauyin kilo 6.142, inda sama da kilo 5 na zinariya mai tsada (18-carat) ne.
Zanen kofin na zamani ne. Duk da shahararsa a duniya, wannan kofin da ake amfani da shi yanzu ya fara ne tun gasar 1974 a Jamus ta Yamma, inda ya maye gurbin tsohon kofin Jules Rimet Trophy bayan Brazil ta lashe gasar sau uku a 1970.
Asalin kofin ba ya fita daga Switzerland. Duk da cewa ƙasashen da suka yi nasara na ɗaukar kofi a matsayin yabo, ainihin kofin zinariya yana nan a ajiye a birnin Zurich, kuma ana fitar da shi ne kawai a lokutan bikin hukuma da gasar kanta.
Zakaru suna karɓar nasu kwafin. ƙasar da ta lashe gasar ba ta riƙe asalin kofin, sai dai tana karɓar wani kwafi mai zinariya da aka yi masa plating, wanda ke zama abin tunawa na dindindin.
Ana rubuta tarihin zakara a jikin kofin. Bayan kowace gasa, ana ƙara sabon faifan ƙarƙashi domin rubuta sunan ƙasar da ta lashe gasar a jikin kofin.
Dokokin taɓa kofin suna da tsauri. Ba kowa ne ke da damar taɓa kofin ba; sai tsoffin zakarun duniya, shugabannin ƙasashe, da manyan jami’an FIFA ne kawai ke iya riƙe shi ba tare da safar hannu ba, yayin da sauran dole su sanya safar hannu don kare zinariyar kofin.
A ƙarshe, kofin Kofin Duniya ba kawai wata kyauta ba ce, alama ce ta ɗaukaka, tarihi da kuma burin da kowane ɗan wasa ke fata ya cimma a rayuwarsa. Yana ɗauke da darajar da ta wuce zinariya—darajar da ke wakiltar mafi girman nasara a duniya ta ƙwallon ƙafa.
