
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Waidi Shaibu ya jagoranci tawagar jagororin tsaro zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato domin duba matakin halin tsaro biyo bayan rikicin da ya ɓarke a kwanan nan da ke nema haddasa fitina ga zaman lafiyar al’umma.
Ziyarar na zuwan ne a daidai lokacin da al’amarin tsaro ke neman taɓarɓarewa a sassan jihar yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan al’amarin domin kauce wa yaɗuwar rikici a faɗin jihar.
A saboda haka ne Laftanal Janar Waidi Shaibu, ya amince da tura ƙarin dakarun soji sama da guda 850 cikin gaggawa domin ƙarfafa tsaro a jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙaruwar hare-haren da ake kai wa fararen hula, musamman harin baya-bayan nan da aka kai a yankin ungwar Rukuba da ke cikin garin Jos ta Arewa, inda mutane aƙalla 28 suka rasa rayukansu.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa (Joint Task Force), Kyaftin Chinonso Oteh, ya tabbatar da cewa waɗannan sabbin dakarun za su taya takwarorinsu da ke sassan jihar wajen kwantar da tarzoma da dawo da doka da oda.
Haka kuma, sojojin za su yi aiki ne a ƙarƙashin wannan runduna ta musamman domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewar acikin al’umma.
A jawabin da ya gabatar a Jos, Janar Waidi Shaibu ya gargaɗe su da su kasance ƙwararru, masu ladabi, kuma su nuna zafi wajen magance ayyukan ɓata-gari da ka iya haddasa fitina.
