Barcelona ta koma matakin farko a kan teburin La Liga, bayan doke Levente 3-0 a wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi.
Kungiyar Camp Nou ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da De Jong da kuma Fermin Lopez.
Da wannan sakamakon Barcelona tana ta ɗaya a kan teburi da maki 60, sai Real Madrid ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani.
Real Madrid ta ci karo da komabaya, sakamakon da ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Osasuna ranar Asabar.
Ranar Laraba, Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Benfica a wasa na biyu a neman cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Champions League.
Wasan farko da suka buga a Portugal, Real ce ta yi nasara a wasan da Vinicius Junior ya yi zargin an yi masa kalaman wariya – UEFA tana bincike kan lamarin.
