Diawara ya soke kwataraginsa da Faransa bayan haramta wa ’yan wasa yin azumi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasar Faransa ta gayyaci Dehmaine Tabibou Assoumani na ƙungiyar Nantes a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan tsakiyar tawagar ’yan ƙasa da shekara 19 ta ƙasar.

Ɗan wasan tsakiyar Mahamadou Diawara ya yanke shawarar barin tawagar ne bayan da hukumar ƙawallon ƙafa ta ƙasar ta kafa wasu sabbin dokoki waɗanda suka haramtawa ‘yan wasa Musulmi yin azumin watan Ramadan a lokacin da suke atisaye.

Diawara bai ji dadin sabbin dokokin ba, waɗanda aka fara aiwatar da su tun daga matakin tawagar ’yan qasa da shekaru 16 har zuwa babbar tawagar ƙasar.

Wannan dalili ne ya sanya Diawara yanke shawarar barin tawagar inda ya koma zuwa ƙungiyarsa ta gida wato Lyon.