Yadda aka sace wani limami a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace babban limamin yankin Iyara da ke Ƙaramar Hukumar Jimu a Jihar Kogi, Sheikh Quasim Musa.

’Yan bindigar sun kai farmaki gidan malamin ne a ranar Litinin 25 ga Maris, 2024, inda suka yi awon gaban da shi kuma har yanzu babu amo ballantana labarinsa.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe, jim kaɗan da isa gidansa da ƙarfe 10 na daren ranar Litinin.

Jami’in hulɗa da jama’a a ƙungiyar ci gaban Iyara, Mista E.K. Adebayo ya ce ’yan bindigar sun afka gidan malamin ne kuma suka yi nasarar awon gaba da shi.

“An sace limamin ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Litinin bayan ya dawo daga Masallaci a ƙofar gidansa da ke Ilukpa a Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.”

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa suna ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da limamin da aka sace.

“Kwamishanan ‘yan sanda a jihar Kogi ya tura tawagar ƙwararru daga sashen ɗaukar matakan gaggawa da mayar da martani tare da ‘yan bangar yankin domin ganin an ceto malamin cikin ƙoshin lafiya,” in ji kakakin.