14
Dec
Dag BASHIR ISAH Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafar nan na ƙasar Brazil, Ronaldo Nazario de Lima, ya yi fatan ƙasar Morocco ta lashe Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Atlas Lions ce ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta taɓa kaiwa matakin na kusa da ƙarshe a tarihin gasar. Morocco ta taki wannan nasarar ce bayan da ta lallasa Portugal da ci ɗaya da nema (1-0) a fafatawar da suka yi a Filin Wasannin Motsa Jiki na Al Thumama da ke Doha. Duk da an yi waje da ƙasarsa Brazil a gasarsa, Ronaldo…