Sifaniya ta hana tawagar Nijeriya bizar zuwa wasanni ƙasarta

Daga MAHDI M. MUH’D

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya, NFF, ta ce Ƙasar Sifaniya ta hana ’yan wasan tawagar Nijeriya ta ‘yan ƙasa da shekara 15 bizar zuwa buga gasa ƙasar.

Ta ce, hana bizar ya shafi ‘yan wasa da jami’an da ke cikin tawagar masu lura da su.

Don haka, “tawagar ba za ta je Sifaniya ba domin buga gasar UEFA ta ‘yan ƙasa da shekara 16,” kamar yadda NFF ta wallafa a shafinta na X.

Sifaniya dai ba ta bayyana dalilin hana bizar ba.

Sai dai hukumomin Sifaniya sun ce dalilin da Hukumar NFF ta bayar na neman bizar bai yi “daidai ba”.

“Jami’inmu da ke Legas ya ce ya bi bayanan mutanen ya ga, waɗanda suka nemi bizar a ranar 8 ga watan Afrilu sun janye buƙatarsu,” kamar yadda wani wakili ya shaida a ofishin jakadancin Sifaniya a Nijeriya.

An tsara Future Eagles za ta bar Nijeriya a ranar Talata domin gasar, kuma za ta fara wasanta na farko da Belgium ne a ranar Juma’a.

Kazalika za ta buga wasa da Ingila da Italiya a gasar.

#

Jerin Manyan Attajiran Nijeriya A 2024
Daga AMINA YUSUF ALI

Wani rahoton sakamakon wani bincike da kafar yada labarai ta Forbes, wacce akasari take kawo ya bayyana sunayen waxanda suka zama attajirai mafiya arziki a Nijeriya a shekarar 2024. Su ne: Aliko Xangote, Mike Adenuga, Abdulsamad Rabiu, da Femi Otedola.
Kafar ta bayyana cewa, arzikin Xangote ya haura zuwa Dalar Amurka biliyan 13.4, na Adenuga ya kai Dalar Amurka biliyan 6.7, yayin da Abdulsalam Rabiu yake da Dala biliyan 5.2 shi kuma Otedola yake da Dalar Amurka biliyan 1.4.
Yadda Xangote ke ciyar da mutum 10,000 kullum a Kano ba ya ga buhun shinkafa miliyan 1 da ya raba
Aliko Xangote shi ne mutumin da ya fi kowa kuxi a Nahiyar Afirka kuma baqar fata mafi arziki a duniya, inda aka kiyasta kudinsa ya kai kusan Dalar Amurka biliyan 13.4 a shekarar 2024. Katafaren kasuwancinsa na rukunnan kamfanin Dangote, na xaya daga cikin manyan kamfanoni masu zaman kansu a Nijeriya kuma kamfani mafi daraja a Afirka ta Yamma.
Shi kuwa Mike Adenuga hamshakqin attajiri xan Nijeriya ya yi shuhura ne da Kamfaninsa na Globacom, kamfanin sadarwa na biyu mafi girma a Nijeriya wanda har ila yau yake da rassa a Ghana da Benin. Haka nan Mike yana da hannun jari a Bankin Equitorial Trust da kamfanin hakar mai na Conoil (wanda a da ake kira Consolidated Oil Company). Forbes ta qiyasta darajar arzikinsa ta kai Dalar Amurka biliyan 6.7 a 2024.
A vangaren Abdulsamad Rabiu, hamshaqin attajirin kuma mai bayar da agaji kuwa, shi ne wanda ya kafa kuma yake shugabantar rukunin kamfanonin BUA Group, wadda ke mai da hankali kan masana’antu, ababen more rayuwa, da noma da kuma samun kuxaxen shiga sama da dala biliyan 2.5.
Femi Otedola hamshaqin dan kasuwa ne a Nijeriya wanda yake shugaban kamfanin Lantarki na Geregu Power Plc. Har ila yau, Otedola ne ya kafa Kamfanin mai na Zenon Petroleum and Gas Limited, kuma shi ne ya mallaki wasu kamfanoni da dama da suke hada-hadar jigilar kayayyaki, gidaje, da kuxi. A baya-bayan nan ya zuba jari a fannin samar da wutar lantarki a wani vangare na ‘yantar da fannin a Nijeriya.
A cewar Forbes, shekara guda kenan da attajiran duniya, wadanda arzikinsu ke ci gaba da tavarvarewa yayin da kasuwannin hada-hadar hannayen jari na duniya ke cikin qa-qa-nika-yi saboda rikicin siyasa, da hauhawar farashin kayayyaki.
“Kamar yadda yake a tsarin tattalin arziki gabaxaya, an fi mayar da hankali ne wurin tattara bayanan kuxi. Yanzu an sami jerin mutane 14 da ke cikin da’irar hamshaqaai da suka mallaki dala biliyan 100, da kuma wasu hamshaqai da arzikinsu ya kai qirgen lambobi 12. Hakan ya kasance ne a kimanin shekara huxu da suka wuce. Waxannan suna daga cikin qalilan da suka taki sa’a, inda darajar arzikinsu ta kai Dalar Amurka tiriliyan 2 gaba xaya, ma’ana kashi 0.5 cikin xari kacal na attajirai 2,781 na duniya da suka mallaki kashi 14 cikin xari na dukiyoyin attajiran da ke doron kasa”. In ji kafar a rahoton da ta fitar.
Kafar ta kuma bayyana cewa, a halin yanzu an samu qarin attajirai fiye da lokutan baya, inda ake da 2,781, an samu karin 141 idan aka kwatanta da yawansu a bara. Arzikinsu ya kai aqalla Dala tiriliyan 14.2 wanda aka samu qarin dala tiriliyan 2 a kan na 2023.
Rahoton kafar ya kuma ayyana cewa Bernard Arnault shi ne ya ci gaba da rike kambunsa na hamshaqin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya. Attajirin mai kasuwancin kayan alatu xan qasar Faransa, an kiyasta yana da Dalar Amurka biliyan 233, inda ya samu qarin dala biliyan 22 a kan abin da ya mallaka a 2023.
Amurka dai ita ce take da tarin hamshaqan attajirai 813 wadanda arzikinsu ya kai Dalar Amurka tiriliyan 5.7, sai qasar Sin da take bi mata da yawan attajirai 473 da suka mallaki Dalar Amurka tiriliyan 1.7.