Yadda yara uku ‘yan gida ɗaya suka riga mu gidan gaskiya rana guda a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Iyalan gidan Malam Sulaiman Ibrahim da ke garin Toto, cikin Ƙaramar Hukumar Toto, Jihar Nasarawa, sun tsinci kansu cikin halin jimami biyo bayan mutuwar wasu yaran gidan su uku wanda mota ta yi ajalinsu a lokaci guda da yammacin Juma’ar da ta gabata.

Yaran da lamarin ya shafa wanda dukkansu mata ne, ‘ya’yan mutum guda ne, kuma ajali ya cim musu ne a hanyarsu ta komawa gida bayan dawowa daga ziyarar gaisuwar sallah.

Maihaifin yaran, Malam Sulaiman Ibrahim, ya yi wa MANHAJA ƙarin haske kan yadda lamarin ya faru inda ya ce, “Lamarin ya faru ne da misalin La’asar na ranar Juma’a a lokacin da yaran ke komawa gida daga yawon sallah.

“Motar da ta buge su ta saki hanya ne ta je ta kwashe su baki ɗaya. Yaran su huɗu ne, uku daga ciki ne nawa, kuma su ɗin ne suka rasu, gudan kuwa ta samu karaya a cinya.

“Da alama direban motar a buge yake da barasa shi ya sa hakan ta faru, domin an samu giya a cikin motar. Kodayake direban ya tsere ba a samu an kama shi ba, amma matasan yankin sun ƙona motar da ya tsere ya bari.

“A nan take yara biyu suka mutu, gudan kuma a asibiti ta cika. Su ke nan yaran da Allah Ya azurta ni da su kuma ga shi Ya karɓi kayanSa a lokaci guda.

“Yaran da lamarin ya shafa su ne; Nusaiba mai shekara 10, Rumasa’au mai shekara 8, sai kuma Maryam mai shekara 6,” in ji mahaifin yaran.

Ya zuwa kammala haɗa wannan rahoton, mahaifin yaran ya ce babu wata hukuma daga yankin da ta shiga lamarin.