Waɗanne ƙasashen Afirka ne suka fi arziki da talauci a 2024? 

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani sakamakon bincike da Bankin ba da Lamun na Duniya ya yi, ya bayyana wasu ƙasashen Afirka mafiya talauci da mafiya arziki a shekarar 2024. A sha karatu lafiya. 

Ana kallon nahiyar Afrika a matsayin wadda ta fi fama da talauci a faɗin duniya, inda abubuwa suka dabaibaye nahiyar kamar yadda tattalin arziki ke tangal-tangal da rashin tsaro da cin hanci da yaƙin basasa da kuma ayyukan ta’addanci.

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar da jerin ƙasashe mafiya arziki da kuma matalauta a faɗin Afrika na shekara ta 2024.

Yayin duba ƙasashe masu arziki a nahiyar Afrika, yana da muhimmanci a duba tattalin arzikin cikin gida, da kuma darajar dukkan kayayyaki da ake samarwa a cikin wannna ƙasa.

Wannan jeri, wanda ya ƙunshi ƙananan kasashe kamar Mauritius da Libya, ya dogara ne akan ƙimar ƙarfin saye, wanda ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki da bambance-bambancen farashin cikin gida, da ba da ingantaccen yanayin rayuwa a waɗannan ƙasashe.

Ga ƙasashe biyar mafiya arziki da kuma biyar mafiya talauci a Afirka a cikin shekara ta 2024 a cewar Bankin Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

  1. Mauritius
    Ƙasar Mauritius na iƙirarin cewa ita ce ƙasa mafi arziki a Afirka a 2024, inda tattalin arzikinta ya kai Dalar Amurka 31,157. Ƙasar wadda aka sani da faɗin tattalin arziki, ta samu nasarar faɗaɗa masana’antunta kamar na sukari da kuma masaƙu.
  2. Libya
    Duk da cewa tana fuskantar ƙalubalen siyasa da tattalin arziki a shekarun baya-bayan nan, Libya ce ta biyu a jerin ƙasashe masu arziki a nahiyar Afrika, inda tattalin arzikinta ya kai Dalar Amurka 26,527. Da farko dai arzikin ƙasar ya dogara ne kan ɗimbin arzikin man da take da shi, kuma ƙoƙarin daidaita tattalin arzikinta ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da riƙe matsayinta a cikin ƙasashe mafiya arziki a Afirka.
  3. Ƙasar Botswana
    Botswana, wadda tattalin arzikinta ya kai dala 20,311, an san ta da irin yadda tattalin arzikinta ke haɓaka da kuma samun nasarar faɗaɗa shi. Ƙasar dai ta sarrafa albarkatunta na lu’u-lu’u yadda ya kamata, tare da zuba jari a fannonin yawon buɗe ido da noma, abin da ya taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikinta.
  4. Gabon
    Gabon wadda ke matsayi ta huɗu, tana da ƙarfin tattalin arziki da ya kai Dalar Amurka 19,865, inda take da ɗimbin albarkatun ƙasa da suka haɗa da mai da kuma ma’adanai. Ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa da gwamnati ta yi da kuma faɗaɗa tattalin arziki ya taka muhimmiyar rawa wajen sanya Gabon a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki a Afirka.
  5. Masar
    Masar tana matsayi na biyar a jerin ƙasashen, inda tattalin arzikinta na cikin gida ya kai $17,786. A matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan al’umma a Afirka, tattalin arzikin Masar yana da girman gaske, inda take da vangarori masu muhimmanci da suka haɗa da yawon buɗe ido, noma da kuma masana’antu.

Mun gama da ƙasashe mafiya arziki yanzu za mu zo kan matalautan qasashe biyar a Afrika. Ga su kamar haka:

  1. Sudan ta Kudu
    Sudan ta Kudu, da ta kasance ƙaramar ƙasa a duniya, ta samu ‘yancin kai a shekara ta 2011. Sai dai tana fuskantar tarin ƙalubale na tattalin arziki. Rikice-rikicen da ƙarancin ababen more rayuwa su ne abubuwan da suka hana ƙasar samun ci gaba. Duk da cewa mutane da yawa sun dogara da noma a ƙasar, tashin hankali da kuma rashin samun ruwan sama na kawo wa harkar ta noma cikas, abin da sa janyo talauci ke ci gaba da yi wa ƙasar mai mutum miliyan goma sha ɗaya wadda kuma ba ta da iyaka da bakin ruwa katutu.
  2. Burundi
    Burundi, wata ƙaramar ƙasa wadda ba ta da iyaka da bakin ruwa da ke Gabashin Afrika, na fuskantar tarin ƙalubale na tattalin arziki da kuma na zamantakewa, ciki har da rashin daidaiton siyasa da tashin hankali da kuma rashin ababen more rayuwa. Taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta da kuma matsin rayuwa da ‘yan ƙasar ke ciki sun faru ne sakamakon ƙaruwar al’ummar ƙasar. Duk da cewa kusan kashi 80 na al’ummar ƙasar sun dogara da noma, ƙarancin abinci da ake fuskanta ya yi katutu idan aka kwatanta da sauran qasashen Afrika da ke Kudu da Hamadar Sahara.
  3. Jamhuriyar Tsakiyar Afrika
    Jamhuriyar Tsakiyar Afrika (CAR), da ke tsakiyar Afrika, na fuskantar halin taɓarɓarewar tattalin arziki saboda rikicin siyasa da ayyukan ‘yan bindiga da kuma rashin ababen more rayuwa. Tattalin arzikin ƙasar ya dogara ne kan zinare da man fetur da sinadarin uranium da kuma lu’u-lu’u. Sai dai duk da wannan ‘yan ƙasar na ci gaba da rayuwa cikin talauci. Hauhawar farashin kayayyaki sakamakon yaƙin da ake yi a Ukraine da ambaliyar ruwa da kuma fari sun ƙara ta’azzara ƙalubalen da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
  4. Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kwango
    Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, ko DRC, ƙasa mafi girma a kudu da hamadar Sahara, na fuskantar manyan ƙalubalen tattalin arziki duk da arzikin da take da shi na albarkatun ƙasa kamar sinadarin cobalt da sinadarin copper. Yawancin jama’a na rayuwa cikin talauci, inda kusan kashi 62 cikin 100 na ‘yan Kongo ke rayuwa a ƙasa da dala 2.15 a rana. Rashin abinci mai gina jiki, ƙarancin damar samun ilimi da na kiwon lafiya, da yawan haihuwa yana ƙara ta’azzara talauci, abin da ya janyo ƙalubale wajen samun ci gaba.
  5. Mozambique
    Mozambique, wadda ba ta da yawan jama’a kuma mai arzikin albarkatun ƙasa wadda Portugal ta yi wa mulkin mallaka, tana fuskantar talauci saboda bala’o’i da cututtuka da ƙaruwar jama’a cikin sauri da ƙarancin amfanin gona, da kuma rashin daidaiton arziki. Duk da arzikin da take da shi da kuma ci gaban arzikin cikin gida, ƙasar na ci gaba da zama a cikin matalautan ƙasashe a duniya, sakamakon hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a yankin arewacin ƙasar mai arzikin iskar gas.