Yadda ɗan almajiri ya fille kan ƙaramin yaro da wuƙa a Kano

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a Jihar Kano sun fara bincike kan badaƙalar fille kan wani ƙaramin yaro mai suna Mohammed Saidu da ake zargin wani ɗan almajiri da aikatawa a ƙauyen Kanwa da ke yankin Ƙaramar Hukumar Madobi a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Usaini Gumel ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) hakan ranar Juma’a a Kano.

Jami’in ya ce ana zargin ɗan al’majirin mai suna Abdullahi mai shekara 16 da kisan Saidu ɗan shekara 6 da haihuwa.

A cewar Gumel, wani mutum ne ya ga Abdullahi wanda ɗan asalin Jihar Zamfara ne a ƙauyen Kanwa ɗauke da wuƙa mai jini a jikinta wanda aka yi zargin jinin na mutum ne.

Da aka matsa da bincike, daga bisani aka gano gangar jikin Saidu a kusa da wata makarantar firamare.

Ya ce daga nan, an ɗauki yaron zuwa gidan mai garin yankin gudun kada fusatattu su auka masa su kashe shi.

Kodayake, ya ce duk ƙoƙarin da aka yi don bai wa yaron kariyar sai da fusatattun matasan yankin suka kutsa suka daki yaron tare da ji masa rauni, in ji Kwamishinan.

Ya ƙara da cewa, ko da ‘yan sanda suka isa wurin, wanda ake zargin ya yi iƙirarin ya fille kan yaron, kuma ya jefa a cikin wata salga da ke kusa da makarantar Firamaren.

Daga nan, ya ce an ɗauki wanda ake zargin zuwa asibitin Kwankwaso don yi masa maganin raunin da aka ji ma sa inda daga bisani rai ya yi halinsa.

Jami’in ya ce an ɗauki gawar yaron da aka fille wa kan zuwa asibiti domin bincike kafin daga bisani aka miƙa gawar ga ‘yan uwanda don binnewa.