Dara ta ci gida: An sace tsohon shugaban ’yan bindiga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gungun mutane sanye da kayan sojoji sun yi garkuwa da wani shahararren tsohon shugaban tsagerun Ribas, High Chief Sobobo Jackrich, wanda aka fi sani da Egberipapa, daga gidansa na Usokun da ke Ƙaramar Hukumar Degema a Jihar Ribas.

Majiyoyi na kusa da tsohon shugaban tsagerun sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidansa ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar ranar Litinin, inda suka kashe wasu hadimansa biyu tare da ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Sai dai ɗaya daga cikin majiyar ta yi imanin cewa sojoji ne suka kai harin, inda ta ƙara da cewa an yi amfani da wasu motoci ɗauke da makamai da suka haɗa da motoci masu sulke wajen aikin.