Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 200, sun tsare 330 a cikin mako guda — DHQ

Daga BASHIR ISAH

Babban Ofishin Tsaro ya bayyana cewa sojoji sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindiga inda sika kashe 188 tare da tsare 330 a yyuka mabambanta fa suka suka aiwatar a sassan Arewa a tsakanin mako guda da ya gabata

Ofishin ya ƙara da cewa, dakarun sun kuɓutar da wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su har mutum 133 a cikin makon.

Daraktan yaɗa labarai, Maj. Gen. Edward Buba, shi ne ya bayyana haka yayin da yake ƙarin haske kan nasarorin da suka samu a baya-bayan nan dangane da yaƙi da ‘yan bindiga a ƙasar.

Sanarwar da ya fitar ta ce, “Sojoji na aiki tuƙuri wajen kakkaɓe ‘yan ta’adda da yaƙi da matsalolin tsaro da kuma tabbatar da tsaron ‘yan ƙasa.

“Kazalika, muna sa ‘yan bindiga na girbar abin da suka shuka. Dakarunmu za su ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a sassan ƙasar nan.

“A tsakanin mako gudan dabya gabata, sosjoji sun kashe ‘yan bindiga 188 sannan sun tsare 330, yayin da suka kuɓutar da 133 waɗanda aka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar.