Ƙarin kuɗin lantarki: Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ya sha alwashin duba lamarin

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya kwantarwa da ’yan Nijeriya hankali kan batun ƙarin farashin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Ben Kalu ya ce ‘yan majalisar sun ƙudiri aniyar tafka muhawara kan ko ya kamata a yi ƙarin kuɗin wutar ko a’a.

A cewar mai magana da yawun Kalu, Levinus Nwabughiogi, ɗan majalisar na amsa tambayar wani mai sauraro da ya yi kiran waya cikin shirin yana tambayar matsayar majalisa kan ƙarin kuxin wutar.

Kalu ya ce, “Gama-garin matsala ce. Ina cikin hutu, amma daga abin da ke damu na akwai takardar da shugaban masu rinjaye na majalisa ya aiko min yana neman mu shiga batun samar da hasken wutar lantarki ga asibitin koyarwa na garin Ibadan.”

“An yanke musu wuta saboda ƙarin kuɗin wutar da aka yi kuma ba su da kuɗin biya.

Benjamin Kalu ya ce ba za su bar ‘yan Nijeriya su sha wahala ba sakamakon ƙarin kuɗin wutar.