EFCC ta ƙwato Naira Biliyan 30 yayin binciken Better Edu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu’annati, EFCC, ta ce ta kwato wa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 30, yayin da ta kuma sanya asusun ajiyar banki 50 a binciken da ake yi wa tsohuwar ministar harkokin jinqai da yaƙi da fatara, Betta Edu da wata ma’aikaciyar ma’aikatar, Halima Shehu.

Kimanin watanni uku da suka gabata ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu da Halima Shehu saboda zargin karkatar da maƙuden kuɗaɗe.

Nan take kuma, Shugaban ya dakatar da shirin na Tallafi da rage talauci (NSIP), sannan ya buƙaci hukumar EFCC da ta binciki jami’an da ke da hannu acikin badaƙalar.

Bayan watanni uku, shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ya bayyana haka, ya ce, hukumar na samun nasarori a binciken.

Olukoye ya bayyana hakan ne a cikin mujallar hukumar da ake fitarwa wata-wata mai suna ‘EFCCAlert’.

“Muna da wasu ayyukan da aka shafe shekara ba a kammala su ba, wannan kuma kun ga makonni shida ne da muka fara bincike a kan lamarin.

“Muna fatan ‘yan Nijeriya za su kara haƙuri, su bamu damar gudanar sahihin bincike tunda yanzu mun kwato Naira Biliyan 30, mun miƙa wa gwamnati.”

Daraktan hukumar ya ce, zuwa yanzu ‘yan Nijeriya sun ga ƙoƙarin da EFCC ke yi, la’akari da adadin mutanen da ake bincike da kuɗaɗe ko kadarorin da aka ƙwato.