Mata ne jaruman watan Ramadan!

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan makon tunatarwar mu za ta mayar da hankali ne kan irin gudunmawar da iyayenmu mata, matanmu na aure, da ƙannenmu mata suke bayarwa a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, wanda a cikinsa mabiya addinin Musulunci a ko’ina a duniya suke gudanar da azumi, da wasu ayyuka na ibada, don neman ƙarin kusanci ga Allah.

Azumi, ɗaya ne daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar wanda Allah Ya farlantawa kowanne mumini, mace ko namiji, don ya kiyaye su a matsayinsa na wanda ya karɓi addinin Musulunci a matsayin hanyar gudanar da rayuwarsa. Don haka musulma mace da musulmi namiji duk suna rayuwa ne a ƙarƙashin dokoki da sharuɗɗan da addinin Musulunci ya gindaya musu, ba tare da nuna wariya ko fifiko ba.

Sai dai bayan dukkan waɗannan dokoki da sharuɗɗan da aka ɗora wa namiji da mace a ƙarƙashin koyarwar addinin Musulunci, mata suna da wasu nauyayan ayyuka da suke gudanarwa da suka sha bamban da na maza, waɗanda za mu iya cewa haqqi ne na zamantakewa da addini. Akasari waɗannan haƙƙoƙi al’adu ne na wajen da suke rayuwa, wanda ke ware wasu ayyuka da hidimomi ga maza da mata. Akwai ayyuka da aka ware da mata ne ya shafa, in aka ga namiji na yi sai ya zama bambarakwai. Haka ma kuma akwai wasu ayyuka da al’ada ta ɗora su a kan maza, waɗanda su ma ba a son ganin mata a wajen.

Ayyuka irinsu girke-girke, da rainon yara, da kwalliya, gyaran ɗaki da sauransu, duk ayyuka ne da mata aka sani suna gudanarwa, saboda yanayin halittar su. Haka kuma aikin da ya shafi ɗaukar ɗawainiyar iyali, ayyukan ƙarfi na ƙwadago, da jagorancin iyali, su ma ayyuka ne da aka fi ɗora su a kan maza, ko da kuwa mata suna iya yi, amma ba a son ganinsu a cikin wannan sabga don ba ta dace da su ba.

Ayyukan shirya girke-girke na abincin buɗe-baki da na sahoor yana ƙaruwa kan mata, bayan sauran ayyukan kula da iyali da suke yi na yau da kullum. Mata ba sa samun lokacin hutawa sosai ko yin barci isasshe cikin dare saboda suna tashi da wuri don fara shirye-shiryen girki ko ɗumamen abincin da za a ci na sahur. A xan tsakanin wannan lokaci ne kuma suke samun yin sallolin nafila ’yan taƙaitattu, saboda rashin isasshen lokaci. Bayan Sahoor suna tsayawa sai sun gyara madafa, sun yi wanke-wanke, da shara kafin su gabatar da sallar asuba, wasu kuma suna yin waɗannan gyare-gyare ne bayan sun gabatar da sallar asuba, saboda lokacin ba shi da yawa.

Ko da sun kammala waɗanan aikace-aikace na Ramadan, idan a ranakun zuwa makaranta ne, kuma suna da ƙananan yara masu zuwa makaranta da safe, sai sun ɗora musu ruwan wanka sun gyara musu jiki, don tafiya karatu. Idan a cikinsu matan akwai masu tafiya makaranta ko rakiyar ’yan makaranta sai sun shirya su ma sun tafi nasu karatun, ko su raka ƙananan, kafin su dawo gida su kwanta su ɗan huta na wasu awoyi.

A kula da kyau matan da suke tafiya wajen aiki ko makaranta da safe, basu da zarafin hutawa da safe, domin kuwa suna gama ayyuka, sai su shirya su ma su fita wajen cigaba da hidimomin da ke gabansu. Haka kuma bayan sun dawo da tsakar rana ko da yamma kusan La’asar za su duƙufa don aikin abincin buɗe-baki. Ka ga ashe ba su da wani lokaci na kansu ko hutawa yadda jikinsu ke buƙata. A irin wannan lokaci hatta biyan buƙatar maigida mata da yawa ba sa iyawa, sakamakon rauni da kasala da suke fuskanta a jikinsu. Idan ba a yi sa’a da miji mai fahimta ba, sai ka ga an fara samun savani, har abin ya nemi kai wa da ɓacin rai.

A daidai lokacin da nake wannan rubutu wasu magidanta sabon aure da ba su wuce watanni uku da aure ba sun rabu, sakamakon samun kansu cikin wata irin rayuwa da ba su saba ba. Rashin haƙuri da rashin tauna kalamin da za a faɗa ya janyo sun yi watsi da tarbiyyar iyaye da nasihohin magabata, sun rusa soyayyar tsawon shekaru da ke tsakaninsu. Wa’iyazubillah!

Lallai a irin wannan lokaci ana buƙatar kai zuciya nesa, da kawar da kai daga wasu kurakurai da za a riƙa gani daga abokan zama, musamman mata, da ake samunsu wani lokaci da rauni wajen riƙe damuwa da danne vacin rai. Idan maigida ya biyewa zafinrai da matsalolin tsadar rayuwar nan da ake fuskanta to, zai yi ta ganin ba daidai ba a wajen iyalinsa, waɗanda su ma suke cikin ƙunci da takura sakamakon rashin samun hutu isasshe da ba sa yi.

Babu shakka mata ba ƙaramin ƙoƙari suke yi ba a wannan lokaci, saboda nauyin aikace-aikace da ke kansu. Dole sai ana haƙuri da su kuma ana rarrashin su, da yaba sadaukarwar da suke yi, sannan za a riƙa ganin abin da ake so. Idan za mu yi musu magana mu yi da tausasawa da amfani da kalmomi masu daɗi, ba cikin fushi, tsawa, ko faɗa ba. Domin hakan shi ne ke sa a ga ba daidai ba, wajen tafiyar da wasu ayyukan.

Wata idan ranta ya vaci ko ta yi girkin ba ya daɗi, saboda za ta riƙa yin aikin cikin rashin jin daɗi. Ko dai a ji gishiri ya yi yawa ko a sa kanwa ta yi yawa, ko kuma a manta ba a sa wani abin da yake ƙara ɗanɗanon girki ba. Sau da dama za ka ji ana zargin cewa ai da gangan ta yi don an mata faɗa. Amma ba lallai hakan ya kasance da gangan ba, sai dai ɓacin ran da ta yi na da nasaba da rashin yin girkin cikin kwanciyar hankali a tsanake.

Sannan yana da muhimmanci a lokacin da maza suke gida suna hutawa cikin watan Ramadan, su riqa taimakawa matansu a cikin gida da wasu ayyuka na shirye-shiryen buɗe-baki, ko da kuwa a madafa ne ko a tsakar gida, yanke-yanken kayan girki, gyare-gyaren wajen da za a zauna a yi buɗe-baki, ko kula da yara a lokacin da kanta ya yi zafi cikin aiki.

Na kalli wani bidiyo na barkwanci da aka nuna yadda mata suke shan aiki a gida lokacin azumi, amma sai ga mijin matar ya mimmiƙe ƙafa a falo yana ta danne-dannen waya, cikin nishaɗi babu abin da ya dame shi. Kuma wannan bai hana ya sa ta yi masa wasu aikace-aikace na daban a cikin gidan ba. Masu wannan bidiyo na nuna halin rashin tausayi da wasu mazan ke nuna wa matansu a irin wannan lokaci na azumin Ramadan. Kuma hannunka mai sanda ne ga maza masu irin wannan hali, don su gane hakan bai dace ba. Taimakawa mata da tausaya musu yana kyau bisa tsari na zamantakewa da koyarwar addini.

Sannan har-wa-yau, yana da kyau ko da wata kyauta ce ta kuɗi ko wani abu da muka san matanmu na so, mu riƙa saya musu muna ba su, don su ji daɗin kyautatawa, kuma su san cewa, ana yabawa da ƙoƙarin da suke yi. Mata mutane ne masu son a yaba musu, kuma a nuna ana jin daɗin abin da suke yi.

Su ma kuma mata su sani cewa wannan aiki da ɗawainiya da suke yi, ibada ce suke yi. Kuma komai ƙanƙantar aikin da suka yi ubangiji yana ninka musu ladan da yake bai wa masu azumi ne, har sau ninkin baninki. Shi ya sa na sanyawa rubutuna na wannan mako taken, ‘Mata Jaruman Watan Ramadan’. Saboda yadda suke samun garaɓasar lada da albarkar ubangiji cikin wannan lokaci. Ina mai yi muku albishir, mata ku sani babu masu morewa da samun lagwadar falala da albarka kamar ku, saboda ku ne jarumai kuma jigon samun nasarar azumin da iyali ke yi.

Babu wanda zai yi azumi ba tare da ya ci abinci ba, kuma duk abincin da za a ci da hannun mata a ciki. Domin kuwa mata su ne iyayen giji!