Mata A Yau

Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Barka da safiya malama Aisha. Na san ba ki san ko wacce ce ni ba, sunana…………kuma na samu number ki ta hannun Hajiya…………ƙawata ce, lokacin da na ke mata bayanin halin da nake ciki ne, sai ta ce, ga number na kira ki, ke ce wadda ki ka zo har gida lokacin da matsalarta da……………..ta yi tsanani, ke ki ka taimaka har aka samu mafita. Malama Aisha, mijina ne can baya shekaru da yawa, shi da wani wan babanshi suka shigo da yamma, wan baban nasa ɗauke da jinjiri, suka ce a Masallacin unguwar…
Read More
Domin ku matan aure

Domin ku matan aure

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja, sannunku da jimirin bibiyar mu. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo ma ku wasu daga ci gaban kayan da za su samar da ni'ima dawamamma ga mace, kuma kayan da ta ke da tabbacin tsafta da lafiyar su, kasancewar ita da kanta ne zata dinga haɗawa. Sai dai kafin nan, zan so in yi amfani da wannan dama in janyo hankalin mata kan illar shan maganin mata da ke bayar da ni'ima ta ɗai rana. Mata ku guji amfani da maganin mata mai bayar…
Read More
Da yawan matan da suka yi kwantai dogon buri ne sila – Fatima Danborno

Da yawan matan da suka yi kwantai dogon buri ne sila – Fatima Danborno

Hana lefe kawai ba zai iya samar da yawaitar yin aure tsakanin matasa ba - Saliha Zariya (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS Idan mai karatu bai manta ba, mun faro tattaunawa kan muhimmancin lefe a Ƙasar Hausa, inda muke tattaunawa da Hajiya Saliha Abubakar Abdullahi Zariya da kuma Fatima Ibrahim Garba Danborno. A wannan satin za mu ɗora ne daga inda muka tsaya: MANHAJA: Wasu na ganin yin lefe kan taimaka wa miji bayan aure, domin ya ɗauke nauyin sutura na tsayin lokaci. Sis Fatima, me za ki iya cewa kan hakan? Yin lefe yana taimaka wa…
Read More
Alaƙar kayan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi

Alaƙar kayan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi

Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin baya mun yi darasi mai tsayi da ya shafi ciwon sanyi, abinda ke kawo shi, ma'anar sa, alamomi da sauransu. Kuma a taƙaice mun faɗa cewa, tushe-tushe, ko saka wasu abubuwa a farji da sunan gyara na iya zama silar gayyatar ciwon sanyi. A wannan satin za mu buɗe wannan darasi da amsa tambayar alaƙar da ke tsakanin kayan mata, ko ince hakin maye ko magungunan ƙarin ni'ima da ciwon sanyi. Idan mun soma da ainahin kayan da ake haɗawa da sunan ƙarawa mace ni'ima, za mu tarar ababe ne da suka haɗa ababe…
Read More
A da neman albarkar aure ya fi yawa a zukatan mutane fiye da yawan lefe – Saliha Zariya

A da neman albarkar aure ya fi yawa a zukatan mutane fiye da yawan lefe – Saliha Zariya

*Lefe yana da kyau, muddin aka karve shi a yadda ya zo - Fatima Ɗanborno Daga AISHA ASAS Kamar yadda muka sani, shafin Gimbiya shafi ne na musamman da ke faɗakar da mata ta ɓangarori da dama, tare kuma da bayyana haƙoƙƙinsu da kuma ilimitar da su kan abinda ya shafi rayuwarsu da kuma zamantakewar aure. Don haka ne ma shafin bai tsaya a iya fira da mata don jin rayuwarsu da hanyoyin da suka bi don samun cigaba tare da ƙalubalen da suka fuskanta don ya zama wata makaranta ga sauran mata ba, domin mukan zaƙulo muhimman ababe ko…
Read More
Dandalin shawara: Ina matuƙar ƙyamar matata a lokacin da ta ke shayarwa

Dandalin shawara: Ina matuƙar ƙyamar matata a lokacin da ta ke shayarwa

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Asas ya yau. Kwana da yawa. Ya iyali. Kin dai san na yi amarya a kwanan baya, kuma kamar yadda muka tattauna a lokaci da yawa Ina matuqar ƙyamar matata lokacin da ta ke shayarwa, dalilin kenan ma da na nemi shawararki a baya, saboda na ce, ba zan iya kusantar matata a lokacin. To yanzu amaryata ta haihu har an yi arba'in, shi ne da sunka yi maganar dawo wa na ce, ta zauna gida tukuna, daga baya ma sai na yi shawarar ta zauna gida har ta yaye jinjirin kana ta dawo. To fa…
Read More
Ya kamata mu jinjinawa ƙoƙarin mata

Ya kamata mu jinjinawa ƙoƙarin mata

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wasu shekaru da suka gabata, tashar rediyon BBC ta taɓa gabatar da wata tambaya ta kacici-kacici mai taken, Wane ne yake da tasiri a rayuwarka? Masu sauraro daga sassan duniya daban-daban sun yi ta bayyana tunane-tunanensu, dangane da wanda suke ganin shi ne ya fi tasiri a rayuwarsu. Wani mai sauraro daga wata ƙasar Turai ya bayyana cewa, matarsa ce ta fi komai tasiri a rayuwarsa, sakamakon ita ce ke sarrafa duk wani abu da ya shafe shi. A lokacin na daɗe ina jinjina wannan magana da mamaki a kanta, mai yiwuwa ƙila saboda…
Read More
Ko motsa jiki na rage ƙiba?

Ko motsa jiki na rage ƙiba?

Daga AISHA ASAS Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake ce da wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar vangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma vangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki wanda lokuta da dama shi ne limamin…
Read More
Tsadar rayuwa: Mata a dinga yi wa maza uzuri

Tsadar rayuwa: Mata a dinga yi wa maza uzuri

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Allah Ya albarkace zuri'armu. A yau dai shafin iyali zai yi jan kunne ne zuwa ga mata, ko in ce rarashi, kasancewar abinda za mu yi magana kansa haƙƙinsu ne a ba su, kuma daidai ne idan sun yi bori yayin da aka hane su. Sai dai masu azancin magana na cewa, "ɗaurowa take a ɗaure alƙali." Yanayi da muka samu kanmu a yanzu ne abin duba ga kowacce mace mai hankali kafin ta zargi mijinta da rashin wadata da haƙoƙin da ya rataya kansa. Halin da muka…
Read More
Mace halitta ce da Allah ya ba wa baiwa ta musamman – Salamatu Bello

Mace halitta ce da Allah ya ba wa baiwa ta musamman – Salamatu Bello

"Kaso saba'in bisa ɗari na mata na taimakon mazajensu a matsalolin gida" (Cigaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, ya ibada? Allah Ya karva, Ya sa mu a bayinSa da zai 'yanta a wannan wata mai daraja. Idan ba mu manta ba, a satin da ya gabata, mun fara tattaunawa da Salamatu Bello Abdullahi, ƙwararriyar 'yar jarida da ke gudanar da shirye-shirye masu ilimintarwa gami da nishaɗantarwa. Mun soma ne da jin tarihin rayuwarta da kuma ƙalubalen da ta fuskata a aikin jarida, sannan mun ja birki kan tambayar da muka…
Read More