Mata A Yau

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (2)

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Masu karatu sannun ku da jimirin karanta wannan fili naku na Zamantakewa, wanda ya ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Kamar yadda muka fara tattaunawa a makon da ya gabata a game da zafin kishin mata da ya addabi al'umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi, to yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A sha karatu lafiya.  Abu na gaba shi ne, ya ke Uwargida ki sani: kasancewarki ta farko a wajensa…
Read More
Namiji mai dukan matarsa

Namiji mai dukan matarsa

Daga AISHA ASAS  Idan an yi zancen namiji mai dukan matarsa a Arewacin Najeriya, ko ma ince a Ƙasar Najeriya bakiɗaya, ba a cika ɗaga kai a dube batun ba, kasancewar ta zama ruwan dare, kuma iyaye da kakani sun mata gurbi a zamantakewar aure, don haka matar da ba ta jure dukan mijinta ana sanya ta a layin marasa haƙuri. Yayin da ka ce duka ba kyau a addinin Musulunci, to fa ka janyo wa kanka abinda za a iya kiranka ɗan tawayen addini, saboda ya yi wa masu yin sa rana. Mazaje da dama suna kafa hujja da…
Read More
Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da jimirin karanta wannan fili namu na Zamantakewa wanda yake zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan zafin kishin mata da ya addabi al'umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi. A sha karatu lafiya.Kafin na shiga rubutun gadan-gadan. Ya kamata na tuna wa 'yanuwana mata cewa: mu ne jinsin da muka fi nuna muna da hadin kai yayin da wata 'yaruwarmu ta shiga wani hali fiye da maza. Kuma mu…
Read More
Matsalar da fyaɗe ke haifarwa ga ‘ya mace

Matsalar da fyaɗe ke haifarwa ga ‘ya mace

Daga AISHA ASAS Kafin komai zan so mu fara da bayyana ma'anar kalmar fyade kafin mu kai ga tattauna matsalolin da ake fuskata bayan fyaden. Fyade wani nau'in cin zarafi ne ta bangaren jima'i, amfani da karfi yayin kusantar mace ko namiji, ma'ana yi ba da amincewar abokin tarayya ba. Idan aka ce fyade, hankalin mutane ya fi tafiya ne ga mata, a ganin su mata ne kawai ake yi wa cin zarafi ta ɓangaren fyade. Ko kaɗan wannan zance ba haka yake ba, domin an tabbatar kaso 29 bisa dari na mazan duniya sun fuskanci cin zarafi ta ɓangaren…
Read More
Abin takaici ne yadda ake samun hannun mata a almundahana – Jamila Tijjani 

Abin takaici ne yadda ake samun hannun mata a almundahana – Jamila Tijjani 

"Taɓarɓarewar tarbiyya daga gida ke samo asali" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Gimbiyarmu ta wannan mako ba kowa ba ce illa Hajiya Jamila Tijjani Abdullahi, tsohuwar lauya, tsohuwar ma'aikaciyar banki, tsohuwar jami'ar gwamnati, malamar makaranta, ƴar kasuwa, kuma mai kishin cigaban rayuwar mata da matasa, kuma shugabar kungiyar Jam'iyyar Matan Arewa a Jihar Filato. 'Ya ce a wajen fitaccen dan siyasar nan na Arewa kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Ambasada Yahaya Kwande. Har-wa-yau, mijinta Alhaji Tijjani Abdullahi, mai lakabi da George Best, tsohon dan siyasa ne kuma babban dan kasuwa a cikin garin Jos. A zantawarta da wakilin Blueprint…
Read More
Basaja a zaman aure (2)

Basaja a zaman aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma'aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi qamari ya kai ga rusa auren gabadaya. A makon da ya gabata mun fara kwararo muku bayani ya zu kuma za mu dora a kashi na biyu na wannan maudu'in. A sha karatu lafiya. Haka su ma mata akwai kawaye da za su dinga cika muku baki…
Read More
Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (4)

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (4)

Daga AISHA ASAS A ci gaba da bayyani kan yadda za a iya ba wa fata kulawa a lokacin sanyi, a yau darasin namu zai tabo bangaren gashi. Sai dai kafin nan zan so mu yi waiwaye don tunatar da mai karatu abinda darasin namu ya kunsa a baya. Mun soma da bayanin yadda fata ke shiga mawuyacin hali a lokutan sanyi, wanda muka ce da taimakon sanin yadda ake iya kula da ita, za a samu sauqi daga irin lalacewar da ta ke yi a lokacin sanyi. Sannan mun kawo hanyoyin da za a iya kula da fatar daga…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya iya gamsar da ni kuma na rasa ta yadda zan sanar da shi

Dandalin shawara: Mijina ba ya iya gamsar da ni kuma na rasa ta yadda zan sanar da shi

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malama barka da rana. An wuni lafiya. Ya iyali. Allah shi taimaka maki, amin. Ni dai tambaya ta dai ina neman yadda zan sanar da mijina ba ya wadatar da ni a shimfida. Wato shi dai mutumin kirki ne sosai, yana iya kar kokari ga iyalinshi, tun ma ba akan abinci ba daidai gwargwado muna ci mu koshi. Yana wasa da dariya da dai sauran abubuwa. To amma matsalar ba shi da wani karfi. Tun da aka kawo ni gidansa a matsayin budurwa babu jimawa na daina koshi da rayya sunnah da muke yi,…
Read More
Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa – Hajara Ɗanyaro

Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa – Hajara Ɗanyaro

"Ina yin shigar mutunci don 'yan baya su koya" Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Daya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a bangaren siyasa, Hajiya Hajara Danyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau. Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye kalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke rike da shi, don haka rayuwarta zata iya zama abin koyi ga…
Read More
Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (3)

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (3)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun kawo yadda za ki iya kula da fatarki, da kuma dabi'un da ya kamata mu dinga yi a lokacin sanyi. A yau za mu tabo wani bangare da ke bukatar kulawa a lokacin sanyi, wato kafa da kuma gashi. A lokacin sanyi ba iya fata ke shiga yanayi ba, asali ma ga wasu kafa ta fi shiga mawuyacin hali fiye da sauran fatar jiki. Kafa wata muhimmiyar vangare ce a jikin mutum da ya kamata a ba ta kulawa ta musamman a lokacin sanyi. Ta yaya za a iya kula da…
Read More