“Kusan duk wani ɗan kasuwa bashi ne babban ƙalubale a gare shi”
Daga AISHA ASAS
Shafin Gimbiya na wannan makon ya zaga ya zagayo, inda ya yi wa masu karatu kamun wata ‘yar ƙwalisa da ta ajiye aiki saboda dalilin kutsawa cikin harkar kasuwancin saye da sayarwa. A ‘yar taƙaitacciyar tattaunawar da Manhaja ta yi da ita, za ku ji yadda ta ba sana’a matuƙar muhimmanci ga kowace ‘ya mace, inda ta kwatanta duk macen da ba ta da sana’ar yi ko yaya take, to tamkar ba ta san ciwon kanta ba ne. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Khadija Ibrahim Madaki:
MANHAJA: An ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, to ko za ki faɗa wa masu karatu taƙaitaccen tarihinki?
KHADIJA: Assalamu alaikum. To ni dai sunana Khadija Ibrahim Madaki, an haifi ne a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ranar 29 ga Janairu, 1977. Na yi makarantar firamare a Maiduguri, wato ‘Shehu Garbai primary school’, daga nan na yi sakandare ɗina a FGGC Potiskum. Sannan na yi jami’a ta a Maiduguri, inda na karanta ‘Sociology and Anthropology’ na kammala a 2007.
To sai na fara aiki da wani kamfanin mai na ‘Gas’ tsawon shekara guda. Bayan nan kuma na yi aiki da gidan rediyon Freedom na Kaduna watanni shida, sannan na zo na yi aiki da kamfanin Dialogue na Kaduna shekara biyu. Daga baya kuma na bari na ci gaba da kasuwanci, ina saye ina sayarwa.
Ba ki sanya batun iyali a cikin tarin na ki ba, ko babu?
Eh gaskiya ba ni da aure.
Allah Ubangiji ya kawo miji nagari. Amma wane irin kasuwanci ki ke yi?
Sana’ar kaya kamar su atamfofi da takalma da kayan ado na mata da irin su zanin gado na zamani da sauran kayayyaki dai kala-kala musamman na mata.
Waɗanne irin nasarori ki ka samu a cikin wannan sana’ar da ki ke yi a yanzu?
Alhamdu lillah! Na samu nasarori da daman gaske, domin ta yi min, ina taimaka wa ‘yan’uwa da iyaye da abokan arziki duk da ita. Sannan kuma ta saka ni mu’amala da dama musamman ma mutanen da ban taɓa tunanin zan yi alaƙa da su ba amman yanzu ga shi mun zama ƙawaye. Ni dai kam ba abin da zan ce sai dai alhamdu lillah.
Waɗanne irin ƙalubale ki ka taɓa fuskanta game da wannan sana’ar da ki ke?
Na fuskanci ƙalubale da dama musamman daga masu biyan kuɗi, domin za mu yi yarjejeniya a kan biyan kuɗi bayan wata uku, amman sai mutum ya yi wata shida bai biya ba. Wani kuma za ku yi maganar biya a sati biyu ko uku, amman sai ranar da ka ga mutum kawai, ƙarshe kuma mutum idan ka matsa ya biya ka kuɗin ka, sai ta kai ma har kun daina magana da mutum a kan kuɗina. A gaskiya wannan shi ne babban ƙalubalen da nake fuskanta a kasuwa ta. Ba ma ni kaɗai ba, kusan duk wani ɗan kasuwa bashi ne babban ƙalubale a gare shi, musamman a ce ka haɗu da masu taurin bashi.
A ina ki ke gudanar da kasuwancin ki, shin akwai wani waje da ki ka ware don gudanar da kasuwancin ki ko kuwa a cikin gida ki ke yi?
Yawanci a cikin gida nake yi, kuma ina ɗorawa a soshiyal midiya irin su Whatsapp, Facebook da Instagram, idan mutum ya gani yana so zai kira ya yi magana ya biya a kai masa ko kuma ya zo da kansa ya amsa.
Wane kira za ki yi ga ‘yan uwa mata na gida waɗanda ba sa sana’a?
Ina kira ga mata ‘yan uwana, rayuwa takan canja, zama kuma zaunewa ne, bai kamata ba a ce mace tana zaune tana jiran miji a kan sai ya yi mata komai, abin dubawa shi ne rayuwa ba ta da tabbas, don haka ‘yan uwa na mata ku tashi tsaye ba wadda za ta rasa sana’ar yi daidai ita, ga sana’o’i nan birjik kala-kala. Ki duba wadda za ki iya.
Idan ki ka ci karo da matan da ba sa sana’a ya ki ke ji a zuciyarki?
A gaskiya nakan tausayawa rayuwar su, domin duk matar da ba ta da sana’a kamar ba ta san ciwon kanta ba ne, wani lokacin ma sukan ban haushi. Kuma ma wannan ma ai kamar rashin kishin kai ne, don kuwa da wannan sana’ar mace za ta taimaki kanta, yaran ta da kuma ‘yan uwan ta, kai har iyaye da miji ma.
Amma wasu matan suna ganin kamar dole sai gwamnati ta sa masu hannu sannan za su yi sana’a. Shin ya ki ke kallon wannan ra’ayi nasu?
A gaskiya wannan ba hujja ba ce, bai kamata ki lanƙwashe hannayenki ba ki ce dole sai kin jira gwamnati ta tallafa miki ko ta baki jarin yin sana’a. Kamar yadda na ce ga sana’o’i nan kala-kala wadda mace za ta iya yi don kare mutuncin kanta. Ba dole sai jari mai yawa ba, ƙarfi-ƙarfi ne abin, idan ba ki da gashin wance, ba dole sai kin yi irin kitson ta ba, za ta yiwu ita ta saba juya manyan kuɗaɗe, tana buƙatar jarin dubu ɗari ko ɗari biyu, ke kuwa jarin dubu biyu ma ya ishe ki, shi ki ke buƙata.
Wanne kira za ki yi ga mata na gida masu zaman jiran miji?
Haƙiƙa jiran miji ganganci ne, mace ko siyan kayan ta yi a wajen ta mijin idan ya dawo ya biya ta ai ta ci gaba. Don rayuwa ta canja sai kana da shi ake yi da kai, don haka mata ku tashi ku taimaki kanku.
To ko akwai wani kira da za ki yi wa gwamnati game da kasuwancin mata?
Alhamdulillah, an zo wajen, haƙiƙa gwamnatoci a kowane ɓangere ya kamata su rinƙa taimakon mata kama da jari da kuma ba su yanayi mai kyau domin gudanar da sana’o’in su, misali kamar yadda za ki ga wasu sun yi hoɓɓasa wajen taimaka wa mata da jari da kuma kayan yin sana’a, to da a ce irin wannan ƙoƙarin dukkan gwamnatoci a kowane ɓangare suna yin koyi da shi da yanzu mata a ƙasar Hausa ko Arewa sun yi nisa. A ƙarshe dai ina kira ga gwamnati da su taimaka wa mata domin idan aka taimake su kamar an taimaki al’umma ne.
Wacce shawara za ki ba mata ‘yan uwan ki?
Shawara ta ga ‘yan uwa mata ita ce, ko wacce mace ya kamata ta rungumi sana’a ganin halin da wannan rayuwa take ciki ayau. Ta hanyar sana’a ce kawai mutum zai taimaki ‘yan uwansa da sauran mutane.
Ya ki ke kallon zurfafa karatu ga ‘ya mace musamman ma karatun boko?
A gaskiya karatun ‘ya mace na da amfani ba ma kaɗan ba; domin da karatun nan ne za ta taimaki iyayenta, ta taimaki mijinta da ‘ya’yanta da kuma ilahirin al’ummar da take tare da su. Ilimin ‘ya mace tamkar haske ne da yake bayyana a ko’ina, kuma kowa zai amfana da shi. Saboda haka yin karatu mai zurfi ga ‘ya mace ko da na zamani ne ba wata illa ba ce, domin idan ba su yi karatun ba ta ya za a samu mata likitoci?
Menene sirrin kwalliya ga ‘ya mace?
To ai ita dama mace da kwalliya aka santa, kuma kwalliya ga ‘ya mace tana da matuƙar muhimmanci, ba wai mace ta caɓa kwalliya a fuska ba ita ce kwalliya, a’a ki kasance mai ado da tsafta da gyara jikinki ita ce kwalliya. Amma idan ba haka ba, ba ma maza ba har mata ‘yan uwanki raina ki za su yi.
Wane abinci ya fi kwanta miki a rai?
ɗanwake.
Wane irin kaya ki ka fi sawa?
Gaskiya na fi ɗaura atamfa, kuma ina son doguwar riga sosai.
Me ke saurin ɓata miki rai?
Ai ni abinda ya fi saurin ɓata min rai shi ne a yi min ƙarya, ko ƙazafi, to wannan abu yana sani takaici sosai.
To me kuma ke saki nishaɗi da farin ciki?
In ga na kasance cikin ‘ya uwana, ma’ana dangi na muna wasa da dariya, ana ba juna labari kala-kala. Har a yi faɗa a dawo a shirya.
To madalla, mun gode.
Ni ma na gode kwarai.
