
Shugaban sojojin saman Nijeriya (NAF), Air Marshal Sunday Aneke, ya ziyarci matuƙa jirgin saman NAF Alpha Jet da suka yi nasarar tsalle daga jirgin kafin ya yi hatsari a ƙauyen da ke yankin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Jirgin ya yi hatsari ne ranar Asabar yayin da ake gudanar da gwajin aiki (post-inspection functional check flight) a sansanin NAF da ke Kainji.
A sanarwar da rundunar sojin saman ta wallafa a Facebook, NAF ta ce ziyarar ta shugaban hafsan sojojin saman na da nufin jinjina jarumtaka, ƙwarewa da hangen nesan matukan a lokacin matsalar da jirgin ya samu a sama.
Aneke ya yaba wa matuƙan, yana mai cewa “dabararsu da gaggawar yanke shawara ce ta hana rasa rayuka ko lalacewar dukiya.”
Shugaban na NAF ya bayar da umarnin gaggauta kafa kwamiti na musamman (Board of Inquiry) domin binciken musabbabin hatsarin.
Rundunar sojin saman ta ƙara da cewa ƙungiyoyin search and rescue, jami’an kashe gobara, da na agajin gaggawa sun isa wurin cikin hanzari domin tabbatar da tsaron matuƙan da kuma kulle yankin hatsarin.
