Gwamnatin Tarayya ta ceto 100 daga cikin ɗaliban Neja da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta yi nasarar ceto ɗalibai guda 100, kamar yadda wata majiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da wani rahoton gida suka bayyana a ranar Lahadi.

Ɗaliban, waɗanda ƴan Makarantar St Mary’s Catholic School Papiri ne na Jihar Neja, za a miƙa su ne ga jami’an ƙaramar hukuma a Neja yau Litinin, a cewar majiyar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Sunday Dare ne ya tabbatar wa AFP batun sako yaran duk da cewa har yanzu akwai wasu guda 165 da ba a san halin da suke ciki ba da suka haɗa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar da lamarin ya rutsa da su.

A kwanakin baya ne cikin watan Nuwamba ƴan bindiga suka yi awon-gaba da mutane 315 a St Mary’s Catholic da suka haɗa da ɗalibai 303 da malamai 12.

Daga bisani jimillar ɗalibai 50 sun yi nasarar tserewa tun ana kwana ɗaya da faruwar al’amarin kuma tuni suka koma cikin iyalansu, inda aka bar guda 265 a hannun ƴan bindigar.

By Babaji