
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa birnin Abidjan na ƙasar Côte d’Ivoire inda zai wakilci Shugaba Bola Tinubu yayin taron rantsar da Shugaba Alassane Ouattara a karo na huɗu a karagar mulki.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya bayyana haka a wata takarda a daren Lahadi wayewar Litinin.
Shettima zai shiga sahun sauran shugabannin ƙasashen Afirka da wasu daga ƙasashen ƙetare da za su halarci taron, wanda za a yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin Abidjan a yau Litinin.
A ranar 25 ga watan Oktoba, 2025 Ouattara ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar, wanda hakan ya ba shi damar cigaba da jagorantar mulkin ƙasar.
Duba da ƙarfin alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da ƙasar ta fuskar difulomasiyya, gwamnatin tarayya na cigaba da ƙoƙarin tallafa wa ƙasashen Afirka ta yamma wajen kiyaye tsare-tsaren dokokin mulki.
Ana sa ran Shettima zai jaddada aniyar gwamnatin Nijeriya ta sadaukar da kai ga ci-gaban martabobin dimukraɗiyya da tabbatar da bin tsarinta wanda shi ne zai kai shiyyar ga nasarori a shugabancinta.
Ƙasashen biyu sun ƙulla alaƙa ne ta ƙungiyoyin ECOWAS da AU musamman akan lamuran tsaro da ci-gaban kasuwanci.
