Tsakanin tausayi da kundin tsarin mulki: Dalilin da ya sa Kotun Koli ta ƙi yafiyar Tinubu ga Maryam Sanda

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Doka mai tsauri ce ke hana aikata laifi, ba tausayi ba – Amina Sidi Aƙibu 

Shekaru da dama, shari’ar Maryam Sanda ta kasance a tsakiyar muhawara mai zafi tsakanin laifi, iko, tausayi da adalci a zuciyar al’ummar Najeriya. A ranar Juma’a, wannan doguwar muhawara ta ɗauki sabon salo bayan Kotun Koli ta Najeriya ta yanke hukuncin da ake ganin shi ne na ƙarshe a ɗaya daga cikin shari’un kisan kai mafi ɗaukar hankali a tarihin ƙasar nan.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda kan kisan mijinta, Bilyaminu Bello, lamarin da ya sake tayar da ƙura a shari’ar da tun da farko ta riga ta raba ra’ayin jama’a. Hukuncin ya zo ne saɓanin matakin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka a baya, inda ya rage mata hukunci bisa dalilan tausayi.

Hukuncin, wanda alƙalai biyar na Kotun Koli suka yanke cikin ra’ayi mabambanta, ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙarar farko da kuma Kotun ɗaukaka ƙara, waɗanda duka suka same ta da laifin kisan kai a shekarar 2017 a gidan aurensu da ke unguwar Maitama, da ke birnin tarayya Abuja.

Da wannan hukunci, Kotun Koli ta soke matakin Shugaban ƙasa da ya mayar da hukuncin kisa zuwa ɗaurin shekaru 12, matakin da aka ɗauka makwanni kaɗan kafin hukuncin ƙarshe na kotu.

An yanke wa Maryam Sanda hukunci a Janairun 2020, bayan shari’ar da ta ɗauki hankalin kasa baki ɗaya, ba wai saboda kisan da kansa ba kawai, har ma da matsayin iyalan da abin ya shafa.

Marigayin mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ne, lamarin da ya sanya shari’ar ke gudana a idon jama’a ba tare da wata boyayyar hanya ba.

Tun bayan da aka yanke mata hukunci, Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru bakwai a gidan gyaran hali na Suleja, inda rahotannin hukumomi suka nuna cewa ta kasance mai kyakkyawan hali, har ma aka bayyana ta a matsayin fursuna abin koyi.

Waɗannan dalilai ne suka zama ginshiƙin yafiyar da Shugaba Tinubu ya yi mata, wadda aka sanar ta hanyar wata sanarwa a jaridar gwamnati, da hannun mai ba shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga. An ce an yi yafiyar ne bisa tausayi, kula da makomar ’ya’yanta, da kuma alamar gyara da ta nuna.

Na ɗan lokaci, al’amura sun nuna kamar shari’ar ta shiga sabon babi, babin tausayi maimakon tsauraran hukunci, wanda wannan babin bai dade ba.

A hukuncinta, Kotun Koli ta kori ƙarar ɗaukaka ƙara da Maryam Sanda ta shigar gaba ɗaya, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifinta ba tare da shakka ba. Babban alƙalin da ya jagoranci hukuncin, Mai shari’a Moore Adumein, ya ce kotunan da suka gabata sun tantance shaidu yadda ya kamata.

“Hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara, wanda ya tabbatar da na kotun sauraron ƙara, ba shi da aibu,” inji kotun.

Abu mafi ɗaukar hankali shi ne yadda Kotun Koli ta soki tsoma bakin shugaban ƙasa kai tsaye. Alƙalan sun ce ɓangaren zartarwa ba shi da ikon yafiya ko rage hukunci a shari’ar da har yanzu ke gaban kotu. A cewarsu, yin hakan na nufin kutsa kai cikin aikin shari’a.

Da wannan mataki daya, Kotun Koli ta dawo da hukuncin asali tare da sake buɗe babbar muhawara ta tsarin mulki: ina ne iyakar tausayi, kuma a ina be dole doka ta tsaya kai tsaye?

Lauyoyi da dama sun yi tsokaci kan hukuncin. Barrista Yusuf AbdulSalam daga Kano ya ce, za a iya kauce wa wannan rigima gaba ɗaya da an ba shugaban kasa shawara mai kyau.

A cewarsa, “Bai kamata a yi yafiya ba kafin shari’a ta ƙare. Idan Kotun Koli ta wanke ta, yafiyar da aka yi da farko ba ta da wani amfani.”

Ya tambayi dalilin gaggawar yin yafiyar, yana mai cewa shugaban ƙasa zai iya umartar Babban Lauyan Tarayya ya janye shari’ar gaba ɗaya (nolle proseƙui), wanda hakan zai bi hanya mafi tsafta ta doka.

A ɓangare guda, Barrista Ronke F. Ajiboye ta ce, hukuncin Kotun Koli, duk da ƙarfinsa a doka, yana haifar da tambayoyin ɗabi’a da na tsarin mulki. Ta ce Sashe na 175 na Kundin Tsarin Mulki ya bai wa shugaban ƙasa ikon yafiya bayan hukunci, tana mai jaddada cewa tausayi wani ɓangare ne na adalci.

Ta kuma nuna damuwa kan tasirin hukuncin ga bil’adama, tana cewa mayar da hukuncin kisa bayan kusan shekaru bakwai a tsare na iya zama hukunci mai tsauri fiye da gyara.

A nashi ɓangaren, Barrista Kelechi Lawrence daga Owerri ya kare hukuncin Kotun Koli, yana mai cewa, ya zama dole domin kare ’yancin kotu da rabon iko tsakanin ɓangarorin gwamnati.

Ya ce, yafiyar shugaban ƙasa ya kamata ta zo bayan kammala shari’a, ba yayin da ƙara ke gaban kotu ba, domin kada a bai wa siyasa damar yin katsalandan cikin shari’a.

A cewarsa, hukuncin ya tabbatar da cewa kowa daidai yake a gaban doka, ba tare da la’akari da matsayi ko kusanci da iko ba.

Shari’ar Maryam Sanda ta wuce zama rigimar shari’a kaɗai. Ta zama madubi da ke nuna rikicin Najeriya da hukuncin kisa, ikon shugaban ƙasa, ƙarfin kotu, da rawar tausayi a adalci na zamani.

Tsakanin tausayin shugaban ƙasa da tsayin daka na Kotun Koli, tambaya ɗaya ta rage: shin adalci hukunci kawai yake bayarwa, ko dole ne ya ba da damar shigar tausayi ko nadama?

A yanzu, doka ta yi magana kai tsaye, karshe, kuma ba tare da sassauci ba. Amma ko tarihi zai kalli wannan tsauri a matsayin cikakken adalci ko rashin tausayi, muhawara ce da ba za ta gushe nan kusa ba.

Da wannan ne shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja ya sake waiwayar jama’a don jin ra’ayoyinsu kan wannan hukuncin.

Idan ba mu manta ba a shekarun baya, Maryam Sanda ta yi matuƙar shahara a cikin ƙanƙanin lokaci, ba kuwa a Arewacin Najeriya ba, ƙasar gaba ɗaya da ma wasu ƙasashen, ba kuwa ta dalilin komai ba face kisan da ta yi wa mijinta uban ‘yar da ta haifa.

Lamarin ya janyo matsanancin tsoro da ya haifar da tambayar ina ne namiji zai iya ɓuya. Duba da yadda matsalar tsaro ke ta’azzara, wanda babu dalili mutum zai iya haɗuwa da ajalinsa a lokacin da ya bar gida, har yake ganin ba lokacin da hankalinsa zai kwanta ya fita daga tsoron farautar ransa kamar idan ya dawo ga iyalinsa.

Da wannan ake ganin kisan da Maryam ta yi a matsayin mafi muni da ban tsoro a cikin dubatan kisan da aka gani ko aka ji labarin aukuwan su a ƙasar nan. Duk da cewa wasu sun waiwayi dalilin wannan ɗanyen aiki da ta aikata, yayin da wasu suka rufe kunnuwansu daga jin dalilin a cewarsu, komai ya aikata bai cancanci kisa daga wadda yake kwana a gado ɗaya da ita ba, wadda suka dunƙule wuri ɗaya da sunan aure ba.

A wata majiya, an ruwaito cewa, Maryam ta kashe mijinta ne dalilin samun ƙwaƙwaran hujja ta samuwar alaƙa ta zina tsakaninshi da mahaifiyarta wadda ta haife ta. Kuma masu wannan ruwayar sun kaffa hujja da ita na za a iya mata uzuri duba da cewa za ta iya aikata hakan ba bisa hayyacinta ba, kamar yadda dokar shari’a ta san da zaman laifin da ake aikatawa a lokacin gushewar hankali ta dalilin kaɗuwa ko razana, wato ‘temporary insanity’ wanda har doka ta kawo sassauci idan hakan ta kasance.

Kan haka ne wasu ke ganin yafiyar Shugana ƙasa ta yi daidai duba da irin halin da take ciki a lokacin da ta yi kisan, kuma suke ganin bai kamata shar’a ta hana aikata hakan ba.

A wani ɓangare an danganta kisan da tsananin kishi wanda ba shi da alaƙa da mahaifiyarta, hakan kuwa zai iya zama wata dama ga sauran mata su kafe da kishi wurin aikata ta’addanci. Hakan ya sa wasu ke ganin ba a buƙatar dalilin da ya sa ta yi kisan, abinda kawai za a duba shi ne kisan da ta yi, wanda yanke hukuncin ne kawai zai sama izna ga matan da za su iya hawa bisa wannan turba. Wato dai bai kamata a sanya tausayi gaba a lokacin yanke hukunci irin na kisa ba.

Kamar yadda wata matashiya, kuma ɗaliba mai karantar likitanci Amina Sidi Aƙibu ta bayyanawa Blueprin Manhaja ra’ayinta kan wannan hukunci da aka yanke wa Maryam Sanda inda ta ce ya yi daidai kuma shi ya dace, duba da irin yadda hankali yake kan shar’ar. A cewarta yafiya ga irin wannan aika-aika ba zai haifar da ɗa mai ido ba agaba, duba da cewa zai iya ƙara wa mata ƙwarin gwiwa kan cika burinsu yayin da kishi ko wani dalili ya auku tsakanisu da mazajensu.

Amina ta ce, “Doka mai tsauri ce ke hana aikata laifi, ba tausayi ba. A shari’ar Maryam Sanda, kiran a nuna tausayi ga wadda aka samu da laifi na iya raunana ƙarfin doka gaba ɗaya. Mutane na bin doka ne saboda sun san hukunci tabbatacce ne, ba wai saboda alƙalan kotu za su iya jin tausayi ko tausayawa masu laifi ba. Idan alƙali ya fara yanke hukunci bisa jinƙai ko tausayi, doka za ta rasa ƙarfinta na hana aikata laifi da tsare al’umma.

A ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasa ne ke da ikon yafiya ko sassauta hukunci ta hanyar clemency, yawanci bayan kotuna sun kammala aikinsu. Alƙalan kotu kuwa, aikinsu shi ne su aiwatar da doka kai tsaye, bisa hujjoji da shaidu da aka gabatar a gaban kotu.

Idan alƙali ya fara nuna jin kai ko sassaucin hukunci saboda tausayi, hakan na nufin ya ƙetare iyakar aikinsa, tare da tayar da rikici a tsarin rabon iko tsakanin ɓangarorin gwamnati.

Idan aka bari tausayi, “kyakkyawan hali,” ko labarin rayuwar mutum su zama ginshiƙin hukunci, to adalci zai koma abin da ya dogara da labarin mutum, ba doka ba. Wannan na iya sa wasu masu laifi su amfana saboda halin da suke ciki, yayin da wasu da suka aikata irin laifin daya su fuskanci hukunci mafi tsauri.

Mayar da hankali sosai kan halayyar mai laifi ko yanayin iyalinta na iya rage darajar rayuwar wanda aka rasa. A shari’ar Maryam Sanda, mutumin da aka kashe — Bilyaminu Bello — shi ne babban wanda aka zalunta.

Adalci na gaskiya dole ne ya fara da girmama haƙƙin wanda aka kashe, ba rage nauyin laifi saboda dalilan tausayi ba.”

Da muka tambaye ta wane darasi wannan rikici na Maryam Sanda ke koyarwa, Amina ta ce, “Rikicin da ya taso a shari’ar Maryam Sanda ya ƙara bayyana dalilin da ya sa alƙalan kotu dole ne su kasance masu tsauri da rashin son zuciya. Tausayi na da matsayinsa a harkar mulki ta hanyar yafiyar shugaban ƙasa, amma ba a cikin yanke hukuncin kotu ba.

Idan alƙali ya aiwatar da doka ba tare da tausayi ba, yana kare fararen hula, yana mutunta haƙƙin wanda aka zalunta, kuma yana hana al’umma faɗawa cikin doka-ta-fi-kowa (lawlessness).”

Ta kuma ƙara da cewa, “adalci ba ya ginuwa kan tausayi, sai kan doka. Idan doka ta tsaya tsayin daka, al’umma za ta samu kariya, tsari da zaman lafiya.”

Da wannan shafin Gimbiya ke jan hankalin ‘yan uwa mata, gani ga wane, ya ishe wani tsoron Allah. Hukunci tare da irin fallasa da Maryam Sanda ta ci karo da shi sakamakon bin son zuciya ya kamata ya zama izna gare ku, ku taushi zuciya yayin mu’amala da mazajenku.

Mun sani cewa mata musamman a Arewacin Najeriya da dama na cikin mawuyacin hali a gidajen mazajensu, suna fuskantar cin zarafi daban-daban daga hannun abokan rayuwarsu, saidai hakan ba yana nufin dama ta aikata kisa ba. Babu wanda ya cancanci ka ɗauki ransa duk girman laifin da ya yi maka.

Ya ke ‘yar uwa, a duk lokacin da ki ka ji zuciyarki ta aminta da ki kashe mijinki akan rinjaye saba’in bisa ɗari, to ki nemi rabuwa da shi shi ne ya fi maki sauƙi akan abinda za ta iya saka ki aikatawa. 

Idan kuma yanzu ta fara kawo maki wannan tunanin ki yi gaggawar fatattakar shi daga cikinta. Musulunci ya ba ki hanyoyin mafita ga auren da ake cin zarafinki ko bakya so, don kada kisa ko makamantasu su samu wata dama a zamantakewar aurenki.

Idan har ba kisa na kare kai ba, wato self defence babu wani dalili da zai halasta maki kashe mijinki don an ba ki damar rabuwa da shi.

Allah Ya mana kariya da zuri’armu baki ɗaya.

By ukarofi