ICPC ta gayyaci Ɗangote kan zargin tsohon shugaban NMDPRA da hannu a rashawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin hanci da Rashawa (ICPC), ta gayyaci Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote domin fara bincike akan zargin da ya yi wa tsohon shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.

Majiyoyi na kusa da al’amarin sun tabbatar da cewa an gayyaci Ɗangote zuwa ofishin hukumar ne inda aka nemi ya je a gobe Litinin ko kuma ya wakilta Lauyansa, wato Ogwu Onoja (SAN) yayin da hukumar ta fara gudanar da cikakken bincike akan ƙorafin nasa.

Ɗangote ya zargi Farouk Ahmed ne da aikata cin hanci da almundahana a lokacin da ya ke kan kujerar shugabancin NMDPRA, zargin da ya janyo hankalin ICPC zuwa ga fara bincike na musamman a kai.

Farouk Ahmed, wanda ya ajiye aikinsa a kwanan nan, ya ce yana maraba da duk wani bincike da za a yi kansa, yana mai cewa hakan dama ce da zai amfani da ita wajen wanke kansa daga duk wata barazana ga sunansa da aikinsa.

A cikin ƙorafin na Ɗangote, ya zargi Farouk Ahmed da rashawa, cin mutuncin aiki da sauya akalar kuɗaɗen al’umma, inda ya yi zargin cewa ya kashe wa ƴaƴansa huɗu jimillar sama da Dala miliyan 7 a karatunsu na sakandare a ƙasar Switzerland, lamarin da Ɗangoten ya bayyana a matsayin abin da ya saɓa wa halastaccen kuɗin shiga na jami’in gwamnati.

A cewar wata majiyar ICPC, hukumar ta nemi Ɗangote da ya gabatar da ƙorafin nasa a hukumance zuwa gare ta tare da hujjojin da za su mara wa zargin nasa baya.

By Babaji