Abin takaici ne yadda iyaye ba sa koyawa ‘ya’yansu iya magana – Safiyya Jibril Abubakar 

Spread the love

“A da iyaye ba su fiye jan ƴaƴa a jiki ba, yanzu kuwa ya zama wajibi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A wannan makon muna ɗauke ne da wata tattaunawa da abokin aikinmu Abba Abubakar Yakubu ya yi da wata fitacciyar malamar makaranta, marubuciya, mai aikin faɗakarwa kan tarbiyya da zamantakewar iyali, ƴar gwagwarmayar kula da haƙƙoƙin marayu da raunana. Safiyyah Jibril Abubakar ƴar Jihar Kaduna, wacce ta kasance jajirtacciyar mace ce mai son ganin an samu sauyin halayya tsakanin manya da yara masu tasowa. Burinta a lokacin tana ƙarama bai wuce ta zama likita ba, sai ga shi a maimakon likitan asibiti, ta zama likitan halayyar al’umma. Haka Allah ke ikonSa. Ga dai Abba nan tare da Safiyya a tattaunawar da suka yi.

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

SAFIYYA: Sunana Safiyya Jibril Abubakar. Ni malamar makaranta ce a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli. Ni masaniya ce a ɓangaren ilimin zurfafa tunani da bincike. Sannan ni marubuciya ce, kuma mai ba da shawarwari kan sha’anin tarbiyyar iyali.

Ki ba mu tarihin rayuwarki da matakin da ki ke na karatu.

An haife ni a garin Kaduna. Na taso a Zariya, inda na yi karatu na zuwa matakin ƙaramar sakandire. Sannan na je karatu a makarantar ƴan mata ta FGGC Gwandu inda na kammala babbar sakandire. Sannan na yi karatun malanta,  a Kwalejin Horar Da Malamai ta FCE Zariya inda na samu shaidar NCE, a ɓangaren koyar da ilimin aikin gona, wato Agric Education. Na yi digirina na farko a fannin koyar da ilimin aikin gona, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Har na koma na fara karatu a fannin ilimin Kimiyyar ƙasa, amma daga baya na ajiye na koma Makarantar Nazarin Harkokin Tsaro ta NDA dake Kaduna, inda na yi digirina na biyu a ɓangaren ilimin Zurfafa Tunani da Bincike, wato Critical and Creative Thinking.

Ba mu labarin yadda ƙuruciyarki ta kasance, wacce tarbiyya ki ka samu yayin tasowarki?

Na taso a gidan malamai, na buɗe ido na ga mahaifina yana koyarwa a Kwalejin Horar da Malamai ta FCE a Zariya, har ya yi ritaya. Mahaifiyata ma malamar sakandire ce. Daga baya ita ma ta koma FCE Zariya tana koyarwa. Ni ce ýa ta hudu a ɗakinmu, mun taso akan turba ɗaya, ina ku ka fito makaranta ina za ku makaranta. ƙa’idar gidanmu ƙarfe huɗu ake tashi da safe, ka yi ibada, ka fara shirin makaranta. Daga makarantar boko kuwa Islamiyya ake wucewa sa an taso ake komawa gida. Nan ma a yi aikin da ake bayarwa na makaranta a yi a gida, wato homework, sannan a yi tilawa, a kwanta ƙarfe tara.

Gidanmu zan iya cewa gida ne na masu tsaurin tarbiyya. Akwai abubuwa da yawa da ko a mafarki ba ka isa ka yi ba, saboda haka dokar gidan take. Misali ba a fita bayan isha’i, don haka mazan gidanmu ba su san zuwa kallon ƙwallo ba.

Wanne buri ki ka taso da shi a rayuwarki?

Babban burin da na taso da shi a rayuwa shi ne in zama likita, in auri lauya, in haifi yara mu dinga larabci a cikin gidanmu. A haka nake hango rayuwata a yayin da na ke tasowa.

Ashe ashe duk mafarkin ido biyu ne.

Me ya ja hankalin ki zuwa ga tarbiyyar iyali da irin gudunmawar da ki ke bayarwa?

Kamar yadda na ce ga buri na, amma a zahiri na iya rubutu, tun daga firamare har na kammala sakandire, na gwanance a Turanci, ina rubutun labari da insha’i da turanci. Ina da nacin son karatu, ba lallai sai a lokacin jarrabawa ba, ina da son karatun littattafan turanci na labari da na faɗakarwa. Sau da yawa yadda mutane ke kallon abu ba haka nake kallo ba, kuma zan dage akan sai na fahimtar da su.

Yaya ki ke kallon tarbiyya a jiya da yau, musamman a nan ƙasar Hausa?

Tarbiyya a jiya ta fi tsauri. Tunanin iyaye a lokacin bai wuce, wannan yarona ne, banbamcinsa da bawa ƴanci ne, ai dole ya bi ni, ai ina da hakki a kansa da sauransu. Ba a kallon ɗa a matsayin mutum ma balle har a tuna yana da hakki a akan iyayensa. Tsaurin ya yi tasirin da iyaye na iya killace ƴaƴansu akan turbar da suke so. Lokacin sai dai a ce aboki ya lalata yaro ko ya na zuga shi. Amma a yanzu da waya a hannu a lokaci daya dubban mutane za su rusa tarbiyyar da ka yi wa yaro. Kenan abin da ya kamata shi ne a yi tarbiyya ana mai ankara da abin da zai iya ɓata tarbiyya. A da iyaye ba su fiye jan ƴaƴa a jiki ba, yanzu kuwa ya zama wajibi.

Ba mu labarin gidauniyarki da ayyukan da ku ke yi?

A shekarar 2012 na buɗe wani zaure a manhajar whatsapp, inda nasa masa suna, Nisa’u Ahlil Jannah. To, daga gida muka fara sauka duk Jumma’a, sai mu haɗa kuɗin sadaka. A haka mu ke kai kayan abinci gidan marayu. A 2015 sai mu ka kai mu ka iske suna da abinci da yawa. A nan ne muka yi shawarar waiwayar iyayen marayu da ke gida. A shekarar muka fara da Ramadan SABIL, inda muke ciyar da marayu da iyayensu. Daga nan muka fara biyan kuɗin makarantar marayu. Daga shekarar ba mu daina ba, don a shekarar 2016  muka yi rijista, sannan muka mayar da hankali wajen biyan kuɗin makarantar marayu.

Yanzu haka muna da waɗanda suka kammala jami’a, akwai wanda ma ya gama da babban sakamako na first class. Bayan kuɗin makaranta muna yi wa marayu ɗinkin kayan sallah, sannan muna rabon abinci da azumi. Kashi sittin cikin ɗari na kuɗin da muke tarawa duk wata, na zuwa ne ga sadakar ga marayu, yayin da sauran ke zuwa ga mabuƙa.

Shin kina ganin tasirin ayyukan faɗakarwar da ku ke yi, musamman a wajen iyaye da alaƙarsu da yaransu?

Sosai ma kuwa. Don ina samun saƙonnin godiya da addu’a daga iyaye.

 Ba mu labarin girman iyalinki da yadda ki ke tsara tarbiyyarsu?

Kamar yadda aka taso da ni, babban abin da na ke nusar da yarana shi ne tsoron Allah.

Sannan na ba su murya, ra’ayin kowa na da muhimmanci ko da a ce ba za a yi amfani da shi ba to, ba za a kushe ba. Muna da dokoki, muna da lokutan yin komai. Ina kuskure, ina gyara kuskuren da na yi idan an nunasshe ni. Ina kuma cigaba da neman ilimi akai, ina ƙoƙarin amfani da shi.

Mene ne babban ƙalubalen iyaye a game da tarbiyyar yaransu?

Rashin sanin wanene su, tsoron kar su gaza. Rashin neman ilimi da son sai sun yi komai daidai, yadda suke so.

Tsakanin yara maza da mata wanne ne tarbiyyar su ta fi ba da wahala?

Ya danganci yadda iyaye suka fuskanci abin, don kowanne ɗa da irin sa. Iyayen da suka natsu suka fahimci ƴaƴansu sun fi samun sauƙin tarbiyya.

Tsakanin malamai da iyaye su waye haƙƙin tarbiyya ya fi nauyi a kansu?

Iyaye. Domin a cikin nauyin har da zaɓa musu malamai nagari, ba waɗanda za su ɗora su a mummunar hanya ba.

Yaya ki ke kallon tasirin kallon finafinai da zaurukan sada zumunta wajen gurɓata tarbiyya?

Abin da muke kallo na da matuƙar tasiri a rayuwar mu, tasirinsa ba lokaci ɗaya yake zuwa ba. Sau da yawa zuwa yake yi ya sauya yadda muke tunani a hankali to, kafin mu farga ya rusa mana tarbiyya ba mu sani ba.

Mene ne ya fi ba ki takaici game da yadda tarbiyyar iyali take a wannan zamani?

Rashin iya magana. Iyaye ba sa koya wa ƴaƴansu iya magana, da ganin daraja mutane. Wasu yaran sam ba su san darajar manya ba, kuma in za su magana yaɓa ta kawai suke yi ba sa tunani.

Idan ki ka haɗu da iyayen yara wacce shawara ki ke ba su?

Su ji tsoron Allah, su sani cewa dukkan ku masu raino ne.

Akwai wani abu da ki ke sha’awar ki ga ana yi a cikin al’umma dangane da gyara makomar matasa manyan gobe?

Buri na in ga an koma kamar da, ana haɗaka a tarbiyya ba wai a bar iyaye da ‘ya’yansu ba.

Game da yadda rayuwar iyaye da matasa take a halin yanzu kina da ƙwarin gwiwa kan cewa rayuwa za ta inganta nan gaba?

Insha Allah, mutuƙar za mu sauya tsarin tunani da mu’amalarmu, a cire son kai a daina fifita abin duniya.

Wanne ƙalubale ko nasara za ki ce kina samu a rayuwarki game da gwagwarmayar da ki ke yi?

Babban ƙalubalena shi ne daidaita tsakanin iyalai da kuma gudanar da aikina. Wani lokaci zan so na yi abu akan lokaci, amma ƙila sai a samu yara ba lafiya, ko kuma abin da za a yi a wajen gari ne, sai ya faɗo lokacin suna makaranta.

Ban da ayyukan gida da na neman halal da ki ke yi, waɗanne abubuwa ki ke yi idan kin keɓe ke kaɗai?

Rubutu, ko karatu, da nazari. Idan na samu lokaci kuma ina da sha’awar kallo.

Jama’a da dama sun sanki a matsayin marubucya, me ya faru yanzu ki ka jingine harkar rubutu?

Ban jingine ba, ka san rubutu na da wani abu, in ka bar shi na wata ɗaya zai barka na shekara. Amma yanzu haka akwai rubutuna da na ke yi, kuma in sha Allahu zai fito a shekarar 2027.

Wanne irin launi ne ya fi baki sha’awa, na sutura ko na wani abu da ki ka fi mu’amala da shi?

Launin Shuni, wato Purple.

Wanne abu ne ya fi ɗaukar hankalinki lokacin da ki ke son yin nishaɗi?

Karatu, da wasanni irin na wasa ƙwaƙwalwa. Ina sha’awar in ga ana wasannin auna basira, ko in yi da yara, ko mu zauna muna hira tare da su.

Idan kin samu dama wacce ƙasa ki ke sha’awar zuwa don hutawa ko yawon buɗe ido?

Saudiyya.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Duk abin da ya kamata a yi, ya kamata a yi shi da kyau. 

Na gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi