Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya ƙaddamar da shirin horas da ma’aikata kimanin 1,800 a kan fasahar kwamfuta, wanda zai gudana na tsawon kwana uku.
Hukumar makarantar KSITM wanda suka ɗauki nauyi gudanar da shirin sun sha alwashin bayar da ingantanccen horo ga ma’aikatan domin zamanan tar da aikin gwamnati a faɗin jihar.
Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da shirin Alhaji Falalu Bawale ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa amfani da fasahar zamani, wanda zai taimaka wajen hanzarta aiki, inganta adana bayanai, da kuma rage dogaro da takardu a ma’aikatun jihar.
Shugaban ma’aikatan ya yi kira ga mahalarta horon da su yi amfani da damar wajen ƙara fasaha da ƙwarewa, domin gwamnati za ta ci gaba da bibiyar yadda horon zai inganta aiki a ma’aikatun su.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina na shirin mayar da jarabawar ƙarin matasayi ta hanyar amfani da kwamfuta ga ma’aikata daga mataki na sha biyar (Level 15) zuwa sama.
Daga ƙarshe ya yaba da yadda ma’aikatan suka nuna sha’awar su na karɓar horo ya kuma yi masu fatan alheri tare da jinjinawa hukumar makarantar KSITM da irin ƙoƙarin da suke wajen bada ingantaccen horo.
A nata jawabin, Dr. Hindatu Abubakar shugabar ɗakin karatu ta makarantar KSITM wadda ta wakilci shugaban makarantar ta tabbatar da cewa an tanadi kayan aiki da kayan koyarwa na zamani domin tabbatar da ingantaccen horo ga ma’aikatan.
Ta ƙara da godiya ga wamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa da ya basu dama na gudanar da wannan horo inda ta sha alwashin tafiyar da shirin yadda ya kamata.
