UNODC ya ayyana Kaduna jihar da ta fi kula da fannin lafiyar ƙwaƙwalwa a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sashen Kula da Lamuran Ƙwayoyi da Manyan Laifuka na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNODC), ya ayyana Kaduna a matsayin madogara wajen kariya ga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da magani a Nijeriya, yana mai jinjina mata bisa manyan matakan gyare-gyaren da ta ɗauka wajen magance matsalolin amfani da miyagun ƙwayoyi da ƙalubalen lafiyar ƙwaƙwalwa acikin al’umma.

A wata takarda da wakilin ofishin na Nijeriya, Cheikh Toure ya fitar zuwa ga Gwamna Uba Sani na Kaduna, UNODC ya yaba wa jihar wajen inganta harkokin fannin a matakin cibiyoyi da yankunan al’umma.

A cewarsa, hakan ya samu ne sakamakon sauyin ci-gaba da jihar ta samu na kafa Hukumar Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun ƙwayoyi da Lafiyar Ƙwaƙwalwa (KadSAMHSA) daga Cibiyar kula da Lamuran Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi.

Ya ce, haɗe ɓangarorin biyu waje guda abu ne da ya yi daidai da yadda ake yi a ƙasashen duniya, wanda ya taimaka wajen samar da kyawawan sakamako.

Haka kuma ya bayyana ƙoƙarin da jihar ke yi wajen lamuran da suka shafi kariya, magani, gyaran hali da wayar da kan al’umma, waɗanda suka samu goyon bayan al’umma sakamakon jajircewar gwamnatin jihar.

Kazalika, sashen ya ce tuni jihohi irin su Yobe, Borno Bayelsa da Kwara suka tuntuɓe shi domin aiwatar da irin tsarin don cimma nasara a yaƙi da ayyukan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da gyaran hali.

Har’ilayau, kasancewar Kaduna ke kan gaba a fannin, UNODC ya yi alƙawarin tallafa wa jihar da kayan aiki da wasu nau’ukan agaji da za su taimaka mata wajen inganta harkokinta ta hanyar ƙulla ƙawancen aiki da KadSAMHSA.

By Babaji